Kungiyar Hamas Ta Ce Falasdinawa Ba Za Su Bar Kasarsu Ba, Ko Da Son Ransu Ko Da Karfi
Published: 20th, March 2025 GMT
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta bada sanarwan cewa mutanen Gaza ba za su taba barin kasarsu ba, da son ransu ko da karfi zuwa wani wuri ba, sai zuwa birnin Qudus babban birnin kasar Falasdinu.
Tashar talabijin ta Presstv ya nakalto kungiyar na fadar haka a jiya Laraba. Ta kuma kara da cewa duk abinda HKI da babbar kawarta Amurka zasu yi don fiddasu daga kasarsu ba zai kai ga nasara ba da yardar All…
Tun shekara 1948 ne kasar Burania a lokacin, wacce ta mamaye kasar Falasdinu ta mikawa yahudawan Sahyoniyya kasar Falasdinu, sannan suka kara mamayar kasar bayan yakin shekara 1967.
Tun lokacin ne Falasdinawa suke gwagwarmaya don kawo karshen mamayar.
A yakin baya-bayan nan dai, wanda aka fara a cikin watan Octoban shekara ta 2023, yahudawan sun kashe falasdinawa kimani 48,000 a gaza kadai, don korar Falasdinawa daga yankin, amma bayan sun kasa korarsu sai aka tsagaita wuta tsakaninsu a cikin watan Jenerun wannan shekarar. Amma a makon da ya gabata yahudawan suka yi watsi da yarjeniyar suka koma yaki da nufin korarsu daga Gaza , a wannan karon tare da taimakon kai Amurka kai tsaye.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Za Ta Kara Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar Zuwa 125%
Duba da cewa, ko a yanzu ma bisa harajin da Amurka ta kakaba, kayayyakin Amurka ba za su iya samun karbuwa a kasuwannin kasar Sin ba, idan har Amurka ta kara yawan haraji kan hajojin Sin, bangaren Sin zai yi watsi da hakan.
Sai dai kuma, idan Amurka ta nace wajen neman illata moriyar kasar Sin, Sin din za ta aiwatar da matakan ramuwa, tare da tunkarar wannan yaki har karshensa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp