Saura Kiris a Samin Tashin Gobarar Tankar Mai a Sakkwato
Published: 20th, March 2025 GMT
An dakile fashewar wata babbar tankar mai a Sokoto bayan da jami’an tsaro da jami’an kwana-kwana da masu bayar da agajin gaggawa suka yi gaggawar kai dauki bayan da tankar ta kife a hanyar Gagi-Nakasari a karamar hukumar Sokoto ta Kudu.
Wani shaidan gani da ido, Magaji Shanono ya shaidawa gidan rediyon Najeriya cewa tankar mai dauke da lita dubu arba’in da biyar na man fetur, ta wuntsila ne a lokacin da take kokarin shiga shatatalen Nakasari, inda ta zubar da mai.
Duk da cewa har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a fitar da wata sanarwa a hukumance ba, sakataren gwamnatin jihar Sokoto Muhammad Bello Sifawa ya halarci wurin da lamarin ya faru, domin ganin abin da ya faru.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sokoto ya kuma sa ido kan matakan tsaro yayin da jami’an kashe gobara suka yi ta kokarin shawo kan lamarin.
Tawagar hadakar hukumar kashe gobara ta tarayya da ta jaha sun isa wurin da gaggawa, inda suka zuba kumfa don kawar da tururin wuta da hana tashin gobara a wajen.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta kasa NEMA da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar SEMA su ma sun wajen don shawo kan cunkoson jama’a, da kuma dakile hadurruka.
Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa jami’an agajin gaggawa sun yi nasarar kwashe man zuwa wata tankar mai, inda suka kawar da illar zubewa ko fashewa.
Jami’an tsaro sun takaita zirga-zirga a wurin da lamarin ya faru, tare da hana mazauna wurin yunkurin diban mai.
NASIR MALALI
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Alhazan Jihar Jigawa Ta Ware Kujeru 54 Ga Malamai Da Jami’an Kananan Hukumomi
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bayyana cewa Gwamna Umar Namadi ya amince da rabon kujeru 54 na Hajj ga malamai da jami’an da za su jagoranci Alhazai don aikin Hajjin 2025.
Babban Daraktan hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga wakilin Radio Nigeria a Dutse, babban birnin jihar.
A cewarsa, Gwamna Umar Namadi ya amince da rabon kujerun ne domin bai wa jami’ai da malamai damar jagorantar Alhzan jihar a Najeriya da Saudiyya.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce, wannan tsari da hukumar ta kirkiro shi ne irinsa na farko a tarihin Jihar Jigawa.
Ya bayyana cewa, an zabi jami’an da malamai maza da mata daga daga kananan hukumomi 27 na jihar bisa cancanta.
Ya jaddada cewa, an zaɓi mutum biyu daga kowace karamar hukuma ta jihar.
Babban Daraktan ya bayyana cewa, malamai da jami’an sun samu umarni don koyar da maniyyata game da wajiban Hajj, ka’idoji da kuma manyan ginshiƙan aikin Hajj domin su san yadda za su gudanar da ibadar Hajj yadda ya kamata.
Ya bayyana cewa, bayar da cikakken horo da ilimantar da maniyyata zai taimaka musu wajen gudanar da Hajj bisa koyarwar addinin Musulunci tare da wakiltar Najeriya da kyau.
Ya ƙara da cewa, za a ci gaba da gudanar da bita ga maniyyatan Hajj na 2025 a dukkan cibiyoyin da aka kebe bayan Ramadan.
Ahmed Labbo ya ce, hukumar za ta fara raba kayayyakin tafiya ga maniyyatan Hajj na 2025 nan ba da daɗewa ba.
A cewarsa, rarraba kayayyakin tafiya wadanda suka haɗa da yunifom da jakunkuna zai fara nan gaba a hedkwatar hukumar da wasu cibiyoyi da aka ware a faɗin kananan hukumomi 27 na jihar.
Ya bayyana cewa, jirgin farko na jigilar maniyyatan jihar zai tashi a watan Mayu 2025 kamar yadda Hukumar Hajj ta Kasa (NAHCON) ta tsara.
Labbo ya jaddada cewa, NAHCON ta ba Max Air damar jigilar maniyyatan jihar zuwa Saudiyya ta filin jirgin sama na Nuhu Muhammadu Sunusi International Airport.
Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazan ya gode wa Gwamna Umar Namadi bisa goyon baya da haɗin kai da yake bai wa hukumar a kowane lokaci.
USMAN MUHAMMAD ZARIA