Gobara Ta Babbake Wani Shago A Jihar Kwara
Published: 20th, March 2025 GMT
Wata gobara da ta tashi da sanyin safiya ta kone wani shago a wani gini mai daki 13 da ke rukunin gidajen Ile-Lodo a cikin garin Etan a karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya fitar, ya ce bayan an samu tashin gobarar ta kira motar kashe gobara da ma’aikatanta sun isa wurin da gaggawa domin shawo kan gobarar, wadda ta kone wani shago a gaban wani gini mai daki 13.
A cewarsa duk da tsananin gobarar, jami’an kashe gobara sun yi taka-tsan-tsan, inda suka dakile tare da kashe wutar kafin ta bazu zuwa wasu gine-ginen da ke kusa.
Sanarwar ta bayyana cewa binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wutar lantarki ce ta haddasa gobarar.
Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Prince Falade John, ya jajanta wa mai shagon da abin ya shafa, ya kuma yi addu’ar Allah ya mayar musu da asarar da suka yi.
Ya kuma jaddada mahimmancin bin matakan tsaro don kaucewa faruwar al’amura a nan gaba.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gobara Kwara kashe gobara
এছাড়াও পড়ুন:
Cutar Sankarau Ta Kashe Mutane 56 A Kebbi
Gwamnatin jihar Kebbi, ta tabbatar da mutuwar mutane 56 a sakamakon barkewar cutar sankarau a jihar inda 25 a Gwandu, 16 a Jega, 14 kuma suka mutu a kananan hukumomin Aliero na jihar.
Da yake zantawa da manema labarai, babban sakatare a ma’aikatar lafiya ta jihar, Dakta Nuhu Koko, ya ce an samu jimillar mutane 653 da ake zargin sun kamu da cutar a kananan hukumomi biyar da suka hada da Aliero, Jega, Gwandu, Birnin Kebbi da Bunza.
A cewarsa, samfurorin da aka aiko da kuma tabbatarwa daga cibiyar bincike, yanzu jihar ta san yadda take magance cututtukan sankarau.
Ya kara da cewa, an aika samfurori 17 zuwa dakin gwaje-gwaje na kasa da kasa da ke Abuja domin tabbatar da su, 5 daga cikinsu sun dawo ba tare da wata matsala ba,5 kuma ba sun tabbatar da cutar ce yayin da Aliero aka samu bullar cutar guda 3, Gwandu 1 da Jega 1.
Dokta Koko ya ce, dukkan majinyatan guda biyar da suka kamu da cutar an yi musu magani kuma an sallame su, yayin da ake jiran sakamakon gwaji guda 7 a NRL Abuja.
Babban Sakatare, ya bayyana cewa, an samu allurai 3,000 na rigakafin CSM daga ma’aikatar lafiya da jin dadin jama’a ta tarayya kuma an rarraba su a fadin kananan hukumomi 3 masu fama da wannan cutar.
Ya bayyana cewa, an samar da cibiyoyin keɓewa tare da haɗin gwiwar MS a Gwandu, Jega da Aliero tare da katifu, magunguna da sauran kayan masarufi da aka samar wa ƙananan hukumomin da abin ya shafa.
COV/Abdullahi Tukur