Sanƙarau ta kashe mutum 55 saboda rashin tsafta a Kebbi
Published: 20th, March 2025 GMT
Aƙalla mutum 55 ne suka rasu sakamakon ɓarkewar cutar sanƙarau a ƙananan hukumomin Jega, Gwandu, Aliero, Bunza, da Birnin Kebbi da ke Jihar Kebbi.
Hukumar Lafiya ta Jihar ta tabbatar da ɓullar cutar bayan gwaje-gwajen da aka yi a Abuja.
Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin ZazzauSakataren Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kebbi, Dokta Nuhu Koko, ya bayyana cewa a Gwandu ne aka fi samun waɗana suka rasu, inda mutum 25 suka rasu, sai Jega da ke 16, sannan Aliero ke da mutum 14 da suka mutu.
Yawancin waɗanda suka rasu sun ɗauka cewa zazzaɓin cizon sauro ne ke damunsu, wanda hakan ya sa ba su garzaya asibiti ba da wuri.
“Ba mu san cewa sanƙarau ce ba. Mutane suna kamuwa da zazzaɓi mai tsanani da ciwon kai, sannan suna mutuwa ba zato ba tsammani,” in ji wani mazaunin Jega, Jafaru Abubakar.
“Wasu na fama da ciwon wuya, wasu kuma suna yin amai sosai kafin su rasu.”
An danganta yaɗuwar cutar da rashin tsafta da cunkoso, musamman a makarantu.
An tabbatar da mutuwar ɗalibai biyar a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliero.
Sai dai duk da haka ba a rufe makarantar ba, amma an mayar da asibitin Jami’ar cibiyar killace marasa lafiya.
Dokta Koko, ya yi gargaɗi kan shan magani ba tare da izinin likita ba, da jinkirta zuwa asibiti, inda ya ce hakan na ƙara yawan mace-mace.
“Yawancin waɗanda suka rasu sun zo asibiti a makare, bayan cutar ta haddasa matsaloli masu tsanani,” in ji shi.
Gwamnatin jihar ta fitar da Naira miliyan 30 don ɗaukar matakan gaggawa, ciki har da raba magunguna, allurar rigakafi, da wayar da kan jama’a.
An shawarci al’umma da su gaggauta zuwa asibiti idan suka ga alamun cutar, su guji shiga cunkoso, tare da kula da tsaftar jiki da muhalli domin daƙile yaɗuwar cutar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwamnati Mutuwa Rashin lafiya Sanƙarau
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 10, Sun Ceto Mutane 101 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina Da Zamfara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp