Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci daukacin masarautun Jihar hudu da su fara shirye-shiryen Bikin Sallah Daba domin ganin jama’a da maziyarta sun ji dadin bukukuwan Sallah.

 

Wannan umarni na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, bayan wani taron buda baki da suka yi da sarakunan gargajiya a dakin taro dake gidan gwamnatin Kano.

 

A cewar sanarwar, gwamna Yusuf ya jaddada cewa al’ummar jihar na zurfafa kallon al’adar sanya sabbin tufafi a ranar Sallah, tare da yin jerin gwano don shaida wa sarakunan su a kan doki, da kuma yin musabaha.

 

Don haka, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba, kuma ba za ta bari wani makiya su tauye wa ‘yan kasa wannan hakki da suke da shi ba.

 

Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa dukkanin hukumomin tsaro a jihar za su ba da himma wajen samar da kariya ga jama’a a yayin bikin.

 

Gwamna Yusuf ya kuma bayyana cewa za a kaddamar da Majalisar Masarautar Jihar Kano a watan Afrilun bana domin samun damar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

 

Gwamnan ya ci gaba da bayyana cewa za a sanar da ka’idojin majalisar,  da sauran muhimman abubuwan da suka shafi majalisar a ranar kaddamarwar.

 

Ya yabawa sarakunan bisa irin balaga da kyakkyawar alaka da suka nuna tun bayan nada su, inda ya ce wannan shi ne karo na farko a tarihin jihar da ake samun kwakkwarar alaka tsakanin sarakunan musamman ta fuskar matsayi.

 

Da yake mayar da jawabi, Shugaban Majalisar Masarautar Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya tabbatar da cewa alakar da ke tsakaninsa da sarakunan masu daraja ta biyu abu ne na musamman.

 

Ya yi kira ga Gwamna Yusuf da ya yi amfani da cibiyoyin gargajiya don yada manufofi da tsare-tsare yadda ya kamata ga al’umma, tare da tabbatar da aiwatar da su cikin inganci.

 

A nasu bangaren, Sarkin Karaye, Muhammad Muhammad Maharaz; Sarkin Rano, Amb. Muhammad Isa Umaru; da mai martaba Sarkin Gaya Dr. Aliyu Ibrahim Abdulkadir a madadin jama’arsu, sun nuna jin dadinsu ga Gwamna Yusuf bisa samar da takin zamani da samar da ababen more rayuwa a fannonin ilimi, lafiya da hanyoyin sadarwa a yankunansu.

 

 

ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Sarakuna Gwamna Yusuf

এছাড়াও পড়ুন:

Wakilin Musamman Na Shugaba Xi Zai Halarci Bikin Rantsar Da Shugabar Namibiya

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Talata cewa, bisa gayyatar da gwamnatin kasar Namibiya ta yi masa, wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Peng Qinghua, zai halarci bikin rantsar da shugabar kasar Netumbo Nandi-Ndaitwah a birnin Windhoek, a ranar 21 ga watan Maris. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Ta Bukaci Taimakon NAMA Don Gudanar Da Aikin Hajjin Bana Cikin Nasara 
  • Gwamnatin Nasarawa Ta Fara Aikin Sabunta Asibitoci 58 Don Inganta Lafiyar Jama’a
  • Fashewar Tankar Man Fetur: Rundunar ‘Yansanda Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutane 6, Motoci 14 Sun Kone A Abuja.
  • Sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano Yayi Alkawarin Inganta Tsaro
  • Sarakunan Kano su kimtsa wa hawan sallah bana — Abba
  • HOTUNA: An yi gobara a kasuwar ’yan gwan-gwan da ke Kano
  • DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen Gwamna
  • Wakilin Musamman Na Shugaba Xi Zai Halarci Bikin Rantsar Da Shugabar Namibiya
  • Wata 11 da tuɓe rawanin wasu sarakuna a Sakkwato