Muhimman ayyuka 8 a goman ƙarshe na Ramadan
Published: 20th, March 2025 GMT
A yayin da aka shiga kwana goman ƙarshe a watan Ramadan, ga tunarwar wasu muhimman ayyukan lada da ya kamata a dage da su a cikin watan mai alfarma.
Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa riƙo da su yana da muhimmanci saboda tarin lada da aka tanadar wa mai aikata su:
Yadda Teloli Ke Cin Kasuwa A Azumin Bana Fursunoni 100 na neman afuwa a Kano Itikafi: Ana so mutum idan mutum yana da hali ana ya shiga Itikafi, inda da lazimci bautar Allah.Mutum, namiji ko mace, na iya Itikafi na tsawon kwanakin ko na iya abin da ya sawwaka. Neman daren Lailatul Kadar: Mutum ya dage wajen kirdado da neman dacewa da daren Lailatul Kadari, ta hanyar gabatar da salloli da addu’o’i da sauran ayyukan ibada, musamman a dararen mara a goman karshen watan Ramadan. Sallah: Musamman Sallar Tarawihi da Tahajjud, baya ga yin sallolin farilla a cikin jam’i, da kuma yin nafilolin da ake yi kafin ko bayan sallolin na farilla. Karatun Al-Kur’ani: A dage a yawaita karatun Al-Kur’ani domin a cikin watan Ramadan aka saukar da shi, a daren Lailatul Kadar, cikin kwana goman karshe. Addu’o’i: A dage da addu’o’in neman garafa da rahamar Allah da aljannah da kuma dacewa da alherin duniya da lahira da kuma neman tsari daga wuta da kuma sharrin duniya da na lahira. Mutum na iya yin addu’a a lokutan da ake amsa addu’o’i kamar lokacin Sahur ko bude-bakin da lokacin da ake cikin azumin da cikin sujada ko a cikin sulusin karshe da dare da sauransu. Umrah: Hadisi ya nuna wanda ya yi Umra a cikin goman karshe na Ramadan zai samu ladar yin aikin Hajji tare da Manzon Allah (SAW). Zakka: Ana so duk Musulmi mai hali ya fitar da Zakkar Kono ya ba wa mabukata. Magidanci da da da hali zai fitar da sa’i daya (Mudun Nabi hudu) na hatsi, haka kuma zai fitar wa iyalansa da duk wanda yake ciyarwa. Ana iya fitarwa a bayar daga ranar 28 ga Ramadan har zuwa lokacin tafiya masallacin idi ranar Karamar Sallah. Kabbarori: Ana yin kabbarori daga bayan faduwar ranar jajibirin Karamar Sallah, har zuwa lokacin da za a idar da sallar idin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Goman Karshe kwana 10 Ramadan
এছাড়াও পড়ুন:
A soma laluben watan Zhul Qi’da — Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya da umarnin fara duban watan Zulki’ida na shekarar 1446 daga gobe Lahadi, 29 ga watan Shawwal, wanda ya yi daidai da 27 ga watan Afrilun 2025.
Hakan na ƙunshe cikin wata takarda da Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin bai wa majalisar Sarkin Musulmi shawara kan harkokin addinin musulunci, Farfesa Sambo Wali Junaid ya raba wa manema labarai.
Sarkin Musulmi ya ce duk wanda ya samu ganin jinjirin watan ya sanarwa hakimi ko uban ƙasa mafi kusa da shi don sanar da majalisar sarkin musulmi.
A ƙarshe sanarwar ta ce Sarkin ya roƙi Allah Ya kawo wa Nijeriya zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa.