Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati
Published: 20th, March 2025 GMT
Sabon Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-ete Ibas (mai ritaya), ya isa jihar domin ci gaba da aiki.
Ibas ya isa filin jirgin saman Fatakwal da misalin ƙarfe 11:25 na safiyar ranar Alhamis inda ya samu tarba daga manyan jami’ai da jami’an tsaro.
’Yan Boko Haram 7 sun miƙa wuya ga sojojin MNJTF a Borno Majalisar wakilai ta amince da dokar ta-ɓaci a RibasSabon Gwamnan, tare da rakiyar Kwamishinan ’yan sandan jihar, Olugbenga Adepoju da mataimakin babban sufeton ’yan sanda na shiyya ta 16, nan take suka wuce gidan gwamnati da ke Fatakwal.
Tuni dai Ibas ya isa gidan gwamnati inda wasu jami’an gwamnati suka zagaya da shi harabar gidan.
A yanzu haka yana ganawar sirri da manyan jami’an tsaro da wakilan gwamnatin tarayya da kuma jami’an gwamnatin jihar.
A ranar Talatar nan ne dai shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya naɗa Ɓice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas a matsayin kantoman jihar Riɓers bayan da ya sanar da ƙaƙaba wa jihar dokar ta-baci. Kuma ya rantsar da shi a ranar Laraba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Asiwaju Bola Tinubu Vice Admiral Ibok ete Ibas an gwamnati
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar wakilai ta amince da dokar ta-ɓaci a Ribas
Majalisar Wakilai ta amince da ayyana dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Jihar Ribas.
Majalisar ta yanke wannan shawara ne a ranar Alhamis, ta hanyar kaɗa ƙuri’a da baki, inda ’yan majalisa 243 suka halarta.
Muhimman ayyuka 8 a goman ƙarshe na Ramadan Fashewar Tanka: Asibitoci sun cika da mutane a AbujaA matsayin wani ɓangare na matakan dokar ta-ɓaci, majalisar ta bayar da shawarar kafa kwamiti domin dawo da zaman lafiya a jihar.
Hakazalika, majalisar za ta karɓi ragamar gudanar da ayyukan Majalisar Dokokin Jihar Ribas na tsawon watanni shida.
Me Ya Sa Aka Ayyana Dokar Ta-ɓaci?Matakin ya biyo bayan rikicin siyasa da ya ƙi ya ƙi cinyewa a Jihar Ribas.
Shugaba Tinubu ya yanke wannan shawara ne sakamakon tashe-tashen hankula da rikicin shugabanci a jihar.
Gwamna Siminalayi Fubara na takun-saƙa da Majalisar Dokokin Jihar da wasu jiga-jigan ’yan siyasa musamman waɗanda ke tsagin tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, lamarin da ya jefa jihar cikin tashin hankali.
Domim shawo kan matsalar, Tinubu ya naɗa Tsohon Babban Hafsan Rundunar Sojin Ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), a matsayin sabon mai kula da jihar.
Hakan ya sa Gwamna Fubara da wasu manyan jami’ai, ciki har da iyalansa, suka bar gidan gwamnatin jihar.
Ana ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki a jihar, yayin da gwamnati ke ƙoƙarin tabbatar da doka da oda a jihar.