Wa Ke Dandana Kudar Matakin Harajin Kwastan Da Gwamnatin Amurka Ta Dauka
Published: 20th, March 2025 GMT
Tun lokacin da Donald Trump ya hau mukaminsa na shugaban kasar Amurka a watan Janairu na bana, sau da dama gwamnatinsa ta dauki matakan kakaba harajin kwastan kan abokan cinikinta. A ganinsa, matakan za su tilasta kamfanoni da su maido da tsarin samar da kayayyaki zuwa Amurka, matakin da zai gaggauta bunkasuwar masana’antun kasar.
Ko abin ya tafi kamar yadda Trump ya yi tsamani?
Alal hakika, manufofi marasa dorewa da gwamnatin Trump ta dauka na illata amanar Amurka, har ma hakan ya yi ta dakushe kwarin gwiwar masu zuba jari na ketare da na kamfanonin cikin gidan kasar. Babban mizanin wasu muhimman hannayen jarin Amurka ya yi matukar raguwa kwanan baya, abin da ya shaida damuwar masu zuba jari a duniya kan rikicin ciniki da tafiyar hawainiya a bangaren bunkasuwar tattalin arziki. Ban da haka kuma, kamfanonin kasar Amurka da kamfanoni masu jarin waje dake kasar za su iya fuskantar hauhawar kudaden kashewa, da katsewar tsarin samar da kayayyaki da dai sauran kalubaloli. A idanun masu zuba jari, Amurka ba ta zama wuri mai inganci na zuba jari a halin yanzu. Ke nan yaya za a kai ga kare masana’antun cikin gidan kasar?
Mun Yi Watsi Da Ayyana Dokar Ta-Ɓaci Da Tinubu Ya Yi A Ribas – Shugabannin Adawa Cikar NUJ Shekaru 70: ‘Yan Jarida Abokan Hulɗa Ne Wajen Aza Kyakkyawar Makoma – Gwamnan GombeBaya ga haka, yanzu al’ummar kasar Amurka na fuskantar hauhawar farashin kayayyaki, har ma bisa nazarin da jami’ar Yale ta yi, an ce ko wane iyalin Amurkawa zai biya karin kudi da yawansa ya kai dala 1600 zuwa 2000 a ko wace shekara, sakamakon karin harajin kwastan da gwamnatin kasar ke bugawa a kan kayayyakin da ake shigar da su daga Mexico, da Canada da Sin.
Kamfanonin dake Amurka da al’ummar kasar, su ne suka fi yin asara karkashin manufar da Trump ya dauka, amma abun tambayar shi ne me ya sa ya yi haka? Kuma wa zai ci gajiyar hakan? (Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Siyo Tan Tan 360 Ga Manoma
Gwamnatin Jihar Jigawa ta siyo tan tan guda 360 domin tallafawa manoma don ci gaba da habbaka harkokin noma a Jihar.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin kaddamar da shirin noman rani na shinkafa a kauyen Jura dake Karamar Hukumar Auyo.
Ya yi bayanin cewar, gwamnatin ta kuma siyo injin girbin shinkafa guda 70 da sauran kayayyakin noma domin tallafawa manoman shinkafa.
A don haka, Gwamna Umar Namadi ya yi gargadin hukunta duk wanda aka samu ya karkatar da kayayyakin aikin gona da gwamnatin ta samarwa manoman jihar.
Yana mai cewar, fiye da manoma dubu hamsin da biyar ne za su amfana da shirin, wanda wani bangare ne na kokarin gwamnati na bunkasa aikin gona da wadata kasa da abinci.
Kazalika, Gwamnan ya kaddamar da rabon Babura 300 ga malaman gona domin wayar da kan manoma.
Ya kuma bayyana irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu wajen bunkasa harkokin noma.
A cewar sa, wannan shirin yana daya daga cikin muhimman manufofi 12 da gwamnatinsa ta sanya a gaba, wadanda suke daidai da manufofin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na samar da wadataccen abinci ga ‘yan Najeriya.
Namadi ya bayyana cewar, tallafawa harkar noma da samar da malamai a fannin gona na daga cikin manyan hanyoyin cimma burin gwamnati na wadatar abinci da habaka tattalin arziki.
Ya kuma yaba da hadin kai da goyon bayan da manoma ke bayarwa wajen aiwatar da irin wadannan shirye-shiryen da gwamnati ke bullowa da su.
Wakilinmu ya bamu rahoton cewar, kananan manoma za su samu rangwamen kashi 30 cikin 100, yayin matsakaita za su amfana da kashi 20, manyan manoma kuma za su samu kashi 10 akan kayayyakin da za su siya.
Kayayyakin da aka raba sun hada da injinan ban ruwa da takin zamani da magungunan kashe kwari da sauran su.
Usman Mohammed Zaria