Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin, da ya mayar da hankali kan karfafa samar da ci gaba mai inganci, da warware tarnakin tafakkuri, da aiwatar da gyare-gyare da kirkire-kirkire, da kokarin ci gaba da azama, da daukar matakai masu inganci, da kuma kafa sabon tushe na ci gabansa a kokarin zamanantar da kasar Sin.

Shugaba Xi, wanda har ila yau yake babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na sojin kasar, ya bayyana hakan ne yayin rangadin da ya kai lardin a ranakun Laraba da Alhamis din nan. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sojojin Kasar Yemen Sun Kai Wa HKI Hari Da Makami Mai Linzami

A ci gaba da taya Falasdinawa fada da sojojin Yemen suke yi, sun kai wa sansanin jiragen sama na HKI dake saharar “Nakab” hari da makami mai linzami samfurin “Ballistic’ wanda ya fi sauti sauri.

A wata sanarwa da sojojin Yemen su ka yi da marecen jiya Talata sun bayyana cewa; a karkashin taimakawa Falasdinawa da ake zalunta, da kuma mayar da martani akan kisan kiyashin da abokan gaba ‘yan sahayoniya suke yi wa ‘yan’uwanmu a Gaza, sojojin Yemen sun kai hari da yardar Allah  akan sansanin sojan sama na Nivatim” da makami mai linzami wanda ya fi sauti sauri, mai suna “Falasdinu 2” sun bisa yardar Allah ya isa inda aka harba shi.”

Sanarwar ta kuma ci gaba da cewa; Sojojin Yemen za su fadada hare-haren da suke kai wa a cikin Falasdinu dake karkashin mamaya a cikin sa’o’i da kuma kwanaki masu zuwa, matukar abokan gaba ba su daina kai wa Gaza hare-hare ba.”

Kakakin sojan Yemen janar Yahya Sari ya kuma bayyana cewa; al’ummar Yemen da ta kunshi jagorori, al’umma da kuma soja, ba za su zama ‘yan kallo ba ana yi wa ‘yan’uwanmu kisan kiyashi a Gaza.” Har ila yau janar Sari ya ce; “ Bisa yardar Allah  sojojin na Yemen za su yi amfani da dukkanin makaman da take da su domin kare da taimakon Falasdinawa da ake zalunta.”

Janar Sari ya kuma ce; Ba za su daina kai hare-haren ba, har zuwa lokacin da za a dakatar da  killace Gaza da ci gaba da kai musu kayan agaji a suke da bukatuwa da su, kuma za su ci gaba da hana jiragen ruwa wucewa zuwa HKI.

A gefe daya, sojojin na Yemen sun sanar da sake kai hari akan jirgin dakon jiragen yaki na Amurka dake cikin tekun “Red Sea” wanda shi ne karo na 4 a cikin sa’o’i 72.

 Janar Sari ya kuma sanar da cewa sun yi nasarar dakile wani hari da ake gab da kai wa Yemen ta sama,kuma hare-haren na Amurka ba za su hana su ci gaba da hana su aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu ba na addini da ‘yan’adamta dangane da al’ummar Falasdinu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Manufofin Kasar Sin Sun Zamo Jagora Ga Duniya A Fannin Kare Hakkokin Bil Adama
  • Kungiyar M-23 Ta Kasar Kongo Ta Kara Nusawa Gaba A Don Mamaye Karin Yankuna A Gabacin Kongo
  • Xi Jinping Ya Yi Rangadi a Birnin Lijiang Na Lardin Yunnan
  • Amurka ce Kadai Ta Ki Yin Allawadai Da Killace Gaza A Tsakanin Mambobin Kwamitin Tsaro na MDD
  • Za Mu Bi Doka Domin Dawo Da Haƙƙinmu – Fubara
  • Sojojin Kasar Yemen Sun Kai Wa HKI Hari Da Makami Mai Linzami
  • Mutum 330 Sun Mutu Yayin da Isra’ila Ta Kai Wa Gaza Sabbin Hare-hare 
  • Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Nacewa Ga Samun Ci Gaba Mai Inganci Yayin Ziyararsa A Guizhou
  • Sayyid Husi: Idan Amurka Ta Ci Gaba Da Kai Mana Hare-hare To Muna Da Hanyoyin Gasa Mata Aya A Hannu