Aminiya:
2025-04-18@03:43:44 GMT

Gobara ta ƙone gidaje tare da asarar dukiya a Gombe

Published: 20th, March 2025 GMT

Wata gobara mai muni ta laƙume gidaje uku a unguwar New GRA, a birinn jihar Gombe, a ranar Laraba inda ta bar iyalai cikin rashin matsuguni tare da asarar dukiya ta miliyoyin Naira.

Waɗanda abin ya shafa sun koka kan rashin damar ceto komai daga kayan su, kuma yanzu haka suna neman tallafin gaggawa domin sake farfaɗowa daga wannan masifa.

‘Za a fara biyan Naira 77,000 ga masu yi wa ƙasa hidima daga Maris’ Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati

Gobarar wadda ta tashi da rana tsaka, ta yi saurin yaɗuwa zuwa gidaje uku, inda ta ƙone su kurmus.

Hukumomin yankin har zuwa yanzu ba su bayyana ainihin dalilin tashin gobarar ba, yayin da waɗanda abin ya shafa suke zaune ba tare da matsuguni ko abinci ko kayayyakin amfani na yau da kullum ba.

Malama Sakina, ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, cikin kuka tana mai bayyana cewa,  “Mun rasa komai. Babu wanda ya taimaka mana lokacin da gobarar ta tashi. Muna buƙatar taimako, musamman daga gwamnati da masu taimakon jama’a, domin mu sake tsayuwa. Kowa ya san halin ƙunci da ake ciki yanzu.”

Wani wanda gobarar ta shafa, Yakubu Baba Gombe, ya bayyana damuwa kan jinkirin da jami’an kashe gobara suka yi wajen isowa wurin. inda ya ce, “Lokacin da suka iso, komai ya riga ya ƙone.”

Iyalan da abin ya shafa yanzu haka sun dogara ne ga taimakon al’umma don samun tallafi na gaggawa. A halin yanzu kuma, mazauna yankin suna kira ga hukumomi da su gudanar da bincike kan lamarin tare da ɗaukar matakan kariya daga aukuwar irin wannan gobarar a nan gaba.

Wakilinmu ya yi ƙoƙarin ya ji ta bakin hukumar kashe gobara kan wannan gobarar amma lamarin ya citura

Wannan iftila’i ya bar mutane cikin baƙin ciki, yayin da iyalai ke roƙon taimako domin sake gina rayuwarsu. Ƙoƙarin jin ta bakin jami’an kashe gobara bai yi nasara ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: tashin gobara da abin ya shafa

এছাড়াও পড়ুন:

Najeriya da gwamnatin sojin Nijar sun sasanta

Gwmanatin Sojin Nijar ta sanar da cewa sun sasanta da gwamnatin Najeriya.

Hakan ta faru ne bayan ziyarar aiki da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya kai birnin Yamai, fadar gwamnatin Nijar.

Bayan sanya hannu kan takardar, Ministan Harkokin Wajen Nijar, Bakary Yaou Sangare, ya bayyana cewa, “da ma Najeriya ’yan uwanmu ne, duk wanda ya ce zai raba  Nijar da Najeriya, shi da kansa ya san ba gaskiya ba ne, abu ne na Allah. Allah Ne Ya haɗa wannan zumunta ka, babu wanda ya isa ya raba ta.”

Takwaransa na Najeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa nan gaba Shugaba Bola Ahmed Tinubu za su gana da shugaban gwamnatin sojin Nijar, Janar Abdurrahman Tchiani, a matsayin ci gaban wannan daidaitawa.

Ya bayyana cewa yarjejeniyar da ƙasashen biyu suka sanya hannu a kai, ta zama, “darasi ga duk wasu ƙasashen duniya, domin yanzu an shiga wani lokaci da ake fama da tashe tashen hankali. To yanzu mu abin da a muka a tsakaninmu ya zama abin koyi.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yawan Kudaden Da Al’ummun Sin Suka Kashe Kan Kayayyakin Masarufi Ya Kai Yuan Triliyan 12.5 A Rubu’in Farko
  • Dangote: Har yanzu gidajen mai ba su rage farashin mai ba
  • NAJERIYA A YAU: Ainihin Abin Da Ke Hana Matan Arewa Koyon Ilimin Kimiyya
  •  Sojojin HKI Suna Ci Gaba Da Kai Hare-hare A Kudancin Lebanon
  • Najeriya da gwamnatin sojin Nijar sun sasanta
  • Ka dawo Najeriya ka magance matsalar tsaro —Obi ga Tinubu
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 7 A Wani Sabon Hari A Benuwe
  • An Kashe Mutane Da Dama A Tsakiyar Najeriya
  •  Aljeriya Ta Kori Jami’an Diflomasiyya Faransa 12
  • An yi garkuwa da masu ibada a Kogi