Sin: Shingayen Kasuwanci Suna Illata Wadatar Tattalin Arzikin Duniya
Published: 20th, March 2025 GMT
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta bayyana cewa, kakaba haraji da sauran shingayen kasuwanci ba za su amfani kowa ba, kuma suna matukar haifar da illa ga samar da wadatar tattalin arzikin duniya, da tafiyar da shi cikin kwanciyar hankali.
Jami’ar wacce ta bayyana haka a yau Alhamis yayin wani taron manema labarai, ta ce kasar Sin za ta ci gaba da kara bude kofa ga kasashen waje, da nuna goyon baya ga ka’idojin ciniki cikin ‘yanci, da tsarin kasuwanci a tsakanin bangarori daban-daban, da karfafa samun moriyar kasa da kasa ta fuskar tattalin arzikin da ya hade kowa da kowa, da neman bunkasa ta bai-daya, tare da samar da moriyar juna da dukkan kasashen duniya.
Mao ta bayyana hakan ne a matsayin martani ga sabon rahoton hasashen tattalin arziki na wucin gadi na kungiyar bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki da ci gaban kasashe ta OECD, wanda ya rage hasashen matakin ci gaban da za a samu a duniya. Rahoton ya yi nuni da cewa, shingayen kasuwanci na baya-bayan nan da wasu kasashe suka kafa na iya kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin duniya, da kuma haifar da hauhawar farashin kayayyaki.
Bugu da kari, a cewar rahotannin kafofin yada labarai, wani dan siyasa a majalisar dokokin Amurka ya aike da wasiku zuwa jami’o’in Amurka shida, inda ya bukaci a bayar da bayanai kan dalibansu Sinawa saboda abin da ya shafi batun “tsaron kasa”. Sai dai, Mao ta bukaci Amurka da ta guji daukar matakan nuna wariya da takura wa daliban kasar Sin. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
OIC ta yi Allah wadai da sake dawo da hare-haren yahudawan sahyuniya a kan a zirin Gaza
Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah wadai da sake dawo da hare-haren wuce gona da irin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tare da yin kira da a dauki matakin gaggawa na kasashen duniya domin dakile wadannan laifuka.
Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi Allah wadai da sake kai hare-haren bama-bamai a yankin zirin Gaza da yahudawan sahyuniya suka yi, lamarin da ya janyo hasarar rayukan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sheik Muhammad bin Abdulkarim Issa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya, ya yi Allah wadai da zaluncin gwamnatin sahyoniyawa, wanda hakan ya saba wa dukkanin dokokin kasa da kasa.
Ya kuma jaddada bukatar daukar matakin gaggawa na kasashen duniya domin dakile wannan kisan kiyashi da mashinan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula da fararen hula.