NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga Sauyin Yanayi Da Lafiyarmu
Published: 21st, March 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Tsawon lokaci, hukumomi a duniya suna gudanar da taruka don nemo hanyoyin daƙile ɗumamar yanayi kan irin illar da ke haifar wa rayuwar al’umma.
Ɗumama ko sauyin yanayi yana barazana ga duniya, yana haifar da sauye-sauye da masana ke cewa zai iya tsananta idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.
Ɗaya daga cikin matsalolin da masana suka gano shi ne sare itatuwa ba tare da dasa sabbi ba, wanda ke illa ga muhalli.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazarin illar sare itatuwa ba tare da dasa wasu ba, da tasirinsa kan sauyin yanayi da kuma lafiyarmu.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: duniya lafiya sare itatuwa Sauyin Yanayi
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya Tana Fatan Samun Dalar Amurka Biliyan $200 A Ayyukan Sararin Samaniya
Gwamnatin tarayyar Najeriya tace tana fatan samun dalar Amurka billiyon $200 a ko wace shekara, a ko wace shekara daga ayyukan sararin samani.
Jaridar Premiun times ta Najeriya ta nakalto ministan kirkire-kirkira da fasahar sararin samaniya yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa kamfanonin sadarwan da suke cikin kasar kamar Starlink da DSTV. Banda haka yace jiragen ruwa masu shigowa kasa ba zasu kaucewa biyan haraji ko kudin foto ba, saboda kayakin aiki na sararin samaniya wanda kasar take da su.
Ministan yace shugaba Tinubu ya bada umurni a yi amfani da fasahar sararin samaniya wajen ayyukan gas da man fetur.
Uche Nnaji ya ce gwamnati tana fatan samun karin dala biliyon 20 a wannan bangaren.