Zargin Kisan Kiristoci A Nijeriya: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da Rahoton Amurka
Published: 21st, March 2025 GMT
Martanin da Fadar Shugaban Kasar ta mayar, ya biyo bayan nuna damuwa a kan matakin da Majalisar Dokokin Amurka ta dauka na amincewa da takunkumin da aka kakaba wa Nijeriya, bisa zargin kashe Kiristoci.
Da yake goyan bayan wannan matsaya, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) reshen Arewa, Rabaran Yakubu Pam ya bayyana a baya bayan nan cewa, abubuwan da suke faruwa na musgunawa Kiristoci, su yi matukar raguwa.
Har ila yau, ya bayyana ci gaban da aka samu, musamman a bangaren wariya ko nuna banbanci ga Kiristoci, wajen mallakar filaye; domin gina Coci-coci da kuma batun tilasta barin addinin da kuma aurar da yara ‘yan mata Kiristoci.
Kazalika, gwamnati ta sake nanata kudirinta na ci gaba da karfafa addinai tare da ba su muhimmanci, inda kuma ta bukaci kungiyoyin kasa da kasa da su yi la’akari da abubuwan da suke faruwa yanzu, maimakon rika dogaro da rahotannin da suka riga suka gabata.
Haka zalika, wata sanarwa da mukaddashin mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ta sanar da LEADERSHIP; ta bayyana damuwarta kan yadda ake faman yada labaran karya da kuma rahotannin bata-gari, dangane da kashe-kashen da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya.
“Wadannan rahotannin karya da shaci fadi, na ci gaba da yin tasiri ga gwamnatocin kasashen waje, musamman ma Gwamnatin Amurka; don ayyana Nijeriya a matsayin kasa mai cin zarafin Kiristoci.
Don haka, Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar, ta bukaci kasashen duniya da su yi taka-tsan-tsan tare da rika tantance bayanai, kafin su kai ga yanke hukunci ko yin kalaman da ka iya tayar da rikici a Nijeriya. “Muna kira ga masu ruwa da tsaki, ciki har da kafafen yada labarai, kungiyin al’umma da kuma abokan huldar kasashen waje; su guji yada labaran da ba su da tabbas a kansu, wadanda za su iya gurgunta zaman lafiya da hadin kan ‘yan kasa”, in ji Ebienfa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Waraka Daga Bashin Ketare
Amfanuwa Da Mamakon Arziki Da A Ka Yi Mana Baiwarsu
Babu shakka, mutuwar zuciya ce ta mai da jama’ar wannan Kasa tamu ta Nijeriya dogara kacokan da sabgar man fetur, a matsayin wata hanya daya tilo da za ta rika samar mana da sama da kashi tamanin ga tattalin arzikinmu na Kasa!. Hakika akwai hanyoyin arzuka iri daban daban cikin wannan Kasa, wadanda ma suka kere fetur sau ninkin ba ninki wajen bunkasar sha’anin tattalin arziki, musamnan sabgar noma, wadda wasu Shekaru can baya, ita ce kashin bayan tattalin arzikin wannan Kasa. Kuma, tun daga wancan lokaci zuwa yau din, harkar noma ce kan gaban fetur, wajen samawa dubban jama’ar Kasa aiyukan-yi.
Yankin arewacin wannan Kasa ta Nijeriya, na daga wuraren da suka fi ko’ina a Duniya kyawon kasar noma. Yankin na arewa, ya fi ko’ina a yankin Afurka ta yamma (West Africa) yawan matattarar ruwa, ko a ce dam dam, wanda ake amfani da su wajen noman rani. Ga dandazon albarkar jama’a da Allah Ya ba mu, wadanda za su wadata wajen noma irin wadannan kyawawan kassai da aka yi mana baiwarsu. Bangaren noman ne ke samawa dubban jama’ar yankin aiyukan-yi sama da komai a ban Kasa, sai dai, shugabanni sun gaza shigowa bangaren na noma, don inganta shi ingantawa.
A Kasar Amurka, Kasar da shugabanni suka shiga harkar tallafar noma kan-jiki kan karfi, ta tabbata cewa, kudin shigar da lemon zaki “Orange” kawai ke samawa Kasar a Shekara, ya fi kudin shigar da gwamnatin Nijeriya ke samu a Shekara wajen man fetur!. Ita kanta Amurkar, ba za ta fada mana ni’imar albarkatun kasa ba, amma sai ga su sun fi mu amfanarsu. Me ya sa? Amsa, shugabanninsu da gaske ne suke, a yunkurinsu na inganta tattalin arzikin Kasar.
Iskar gas kawai da Allah Yai wa Nijeriya baiwarsa, zai iya daukar nauyin bai wa daukacin nahiyar Afurka da ke kunshe da Kasashe 52 ko 53 wajen sama musu wadatacciyar iskar gas. To Amma dan Nijeriya a yau, nawa ne yake shan litar gas? Da kuma mai karatu zai lalubi wasu Kasashe cikin Duniya da ko kama kafarmu ba su yi ba wajen mallakar iskar gas din, sai ya samu kuma sun fi mu shan gas din da arha!. Wadanne irin shugabanni muke da su ne? Eh mana, tun da sarrafawa da inganta harkar gas din, na hannunsu ne.
Misali mutum ya ce fetur, gas, rake, lemo da makamantansu, za a ga an ba mu albarkatun kasa na abubuwa daidai har sama dari biyu da hamsin (250) iri daban daban. Cikin wadannan albarkatun kasa akwai bishiyar Katako, wani masani ke cewa, da Nijeriya za ta inganta bishiyoyin Katako da take da su, su kadai, za su iya zama abin dogara kamar man fetur, kuma su rike Kasar. Wane shiri ne a kasa a yau da mutanen wannan Kasa za su ce sun ga gwamnati na yi, don inganta sabgar bishiyoyin Katakonta?
Mutum ya dauki gyada kawai, zai yi matukar mamakin irin tattalin arzikin da ke kunshe cikinta. Daga gyada, akwai sinadaran da ake yin sabulu, abin yin biskit, abin yin abincin dabbobi, abincin kifi, abincin kaji da sauransu. Ka da mai karatu ya mance da man girki da ake samu daga gyadar. Ko mai karatu ya san da cewa a na yin makarin inji daga matsanancin hucin zafi, wanda a turance ake kira da “engine gasket” da bawon gyadar? To amma a yau, wane hobasa ne na hakika ba na baka ba, da za a ce gwamnatocinmu na yi, don ganin mun amfana hakikar amfanuwa daga mamakon tattalin arziki da ke kunshe cikin gyada?
Cikin wata budaddiyar wasika da Dattijo, Alhaji Dattijo Adhama ya rubuta zuwa ga hukumomi masu gudanarwa da masu yin doka na arewacin wannan kasar, “An Open Letter To The Northan Edecutibes & Legislatures” a Watan Yulin Shekarar 2021 (July, 2021), da mutum zai duba shafi na biyar (P5) na wannan wasika, zai amfana da wata irin kididdiga da aka yi, wadda ta nuna irin biliyoyin kudaden da jihar Kano za ta iya samu a kullum daga man gyadar da za a sha a cikin jihar. Cikin kididdigar, an nuna cewa, jihar ta Kano na iya samun kudin shiga sama da naira biliyan saba’in da biyu (N72b) a kullum. Da sharadin, wancan bangare na masu zartarwa da masu doka sun shigo sun gama kai wajeguda, tare da datse shigowar man gyadar daga Kasashen ketare, ta hanyar yin doka a Majalisa.
A tsakanin garin Makoda da Dambatta, akwai wani nau’in yashi da Kasar China ke ta begen ganin ta sami kai wa ga tononsa, don sana’anta gilashi da shi. Duk cikar Kasar ta China, ba su da wani ma’adin yin gilashi sama da irin wannan yashi na tsakanin Dambatta da Makoda. Idan ban manta ba, wani lokaci can baya, ta hanyar Malam Gambo, shugaban ma’aikata “Staff Officer” na Kasuwar Sabon Gari, ya gabatar min da shugabancin masu harkar gilashi ta Kasuwar Kofar Ruwa, na wuce gaba zuwa kai kuka ga Sanatan yankin, Barau Jibril”, da zimmar ya wuce musu gaba wajen tono yashin, amma lamarin ya gagari kundila.
Ba sai Kano ba, muddin mai karatu dan Nijeriya ne, ba zai gaza tunanin wani ma’adin ko albarkar Kasa da Allah Ya hore musu a yankinsu ba. Babbar matsalar a yau ita ce, masu mulki ba su damu da hako ko amfanar da jama’ar Kasa daga irin wadancan amfanoni da Allah Yai mana baiwarsu ba. Sai ma aka wayigari, idan akwai wani ma’adani a waje, sai a sami wasu marasa kishin kasa su game baki da Turawa, a zo a haddasa mummunar fitinar da za ta kai ga kashe rayukan dubban jama’a a wajen. Bayan kowa ya yi kaura ya yi gudun tsira da ransa, sai wadancan marasa kishin kasa da bakin haure su dukufa kwasar wadancan ma’adanai, shin, me ke faruwa a Zamfara a yau?
Duk irin albarkatun kasa da aka yi wa wata Kasa baiwarsa a Duniya, muddin shugabanninta ba sa kishinta, to fa a banza, ba za su amfana ba. Kuma ba za a bar su su zauna lafiya ba.
Da shugabanni a Nijeriya za su karkata ga sabgar noma kadai, su zuba jari ciki, su samawa manoman taki da kasuwa, babu shakka da an fita daga wannan kagaggen talaucin da aka jefa jama’ar wannan Kasa ciki. Talaucin Kasar Nijeriya ba daga ne yake ba, tun da Allahn Ya ba da mafita.
Samar Da Gungun Masana Masu Kishin Kasa
Dole ne gwamnati ta yi zabarin manyan mutane masana gogaggu, wadanda lamarin Kasar ne ke kunshe cikin zukatansu sabanin muradansu na son zuciya. Hakika Allah Yai mana baiwar mutane hazikai masana, wadanda hatta sassan Kasashen Duniya ke daukarsu aikin dindindin da na kwantaragi, don inganta harkokin Kasashen nasu. Dole ne a lalube su, a saurari shawarwarinsu, a dabbaka abubuwan da za su gabatar a matsayin shawara ko a matsayin wani sharadin da wajibi ne binsa, wajen inganta harkokin tattalin arzikin namu, muddin a na son A’i ta fita daga rogo ba tare da ta karce jiki ba.
Lokacin da marigayi Umar Musa ‘yar’adua ya tasamma yin gyara game da sha’anin Zabe a Nijeriya, ya kafa wani babban Kwamiti ne a karkashin tsohon babban Joji na Kasa Uwaisu, da sauran masu kishin kasa, mutane irinsu Farfesa Attahiru Muhammad Jega, OFR, ai sanin kowane cewa, a karshe, laya ta yi kyawon rufi. Gwamnati ba ta yi wa kwamitin wani katsa-landan ba, sannan kuma ta tasamma dabbaka irin shawarwarin da wancan kwamitin ya gabatar mata. Bugu da kari, gwamnati ta dauko guda daga cikin ‘yan kwamitin, Jega, ta danka hukumar zaben Kasar kacokan a hannunsa, hakan ne ya jaza aiwatar da zabukan da ba a taba samun masu ingancinsu ba cikin tarihin Zabukan Kasar gabaninsu, wato Zabukan Shekarun 2011 da na 2015, kamar yadda masana da sauran masu sanya idanu na gida da waje suka fadi.
Ko da an kafa wani kwamiti na masana kuma masu kishin kasar, muddin za a yi musu katsa-landan cikin sabgar kwamitin, ko kuwa, shawarwarin da suka gabatar, a yi wurgi da su, to fa babu inda za a je, sai dai kawai a ci gaba ne da tsalle a wajeguda kamar yadda aka saba.
Duk kyawon wani kwamiti da sunan gyara tattalin arzikin Kasa da aka kafa, ko za a kafa ba bisa cikakkiyar cancanta ba, shi ma ba zai cimma komai ba mai alfanu, lamura za su ci gaba da wakana ne cikin yanayi na daben-kwalo.
Duk karatu da Dr Abel Guobadia da Professor Maurice Iwu ke da, ba su jagorantar Hukumar Zabe, INEC, ta Kasa da aka yi bisa wata manufa, a karshen lamarin, sun gudanar da wasu nau’ikan Zabuka ne gurbatattu, wadanda gabaninsu a Kasar, ba a taba cin karo da miyagun Zabukan irinsu ba!.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp