Tunisiya : Kaïs Saïed, ya kori firaministansa Kamel Madouri
Published: 21st, March 2025 GMT
Shugaba Kaïs Saïed na Tunisiya ya kori firaministan kasar Kamel Madouri, da aka nada a watan Agustan da ya gabata yayin wani gagarumin garanbawul a majalisar ministocin kasar a daren jiya Alhamis.
Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce an maye gurbin firaministan kasar Madouri nan take inda aka maye gurbinsa da Sarra Zaafrani Zenzri, ministar kayan aiki.
Sanarwar ta ce sauren mambobin gwamnatin zasu ci gaba da aikinsu.
Garan bawul na shugaban kasar ta Tunisia a baya baya nan shi ne na ranar 6 ga watan Fabrairu inda ya sallami ministan kudinsa Sihem Boughdiri Nemsia da tsakar dare, tare da maye gurbinsa da alkalin kotun Michket Slama Khaldi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Macron : Faransa na shirin amincewa da yankin Falasdinawa a matsayin kasa
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya ce kasarsa na shirin amincewa da yankin Falasdinawa a matsayin kasa nan da watanni masu zuwa.
Ya ce hakan na iya faruwa a farkon watan Yuni nan wannan shekarar a taron Majalisar Dinkin Duniya da za a gudanar a New York.
kawo yanzu, Kasashe 147 ne suka amince da yankin na Falasdinawa a matsayin kasa mai yanci.
Kasashen Sifaniya da Ireland da Norway su ne na baya-bayan nan da suka nuna amincewarsu a watan Mayun bara da yankin na Falasdinawa a matsayin kasa mai yanci, matakin da ya fusata Isra’ila.
Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa da dama dai na ganin samar da kasashe guda biyu Falasdinu da Isra’ila shi ne gimshikin samar da zaman lafiya a yankin.