Cibiyar Bincike Kan Harkar Noma (IAR) tare da hadin gwiwar Hukumar Yada Sakamakon Bincike da Wayar da Kan Manoma ta Kasa (NAERLS), Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, sun shirya taron kwana guda a Kaduna domin masu ruwa da tsaki kan aikin bunkasa noman dawa a Najeriya.

 

Taken taron shi ne: “Gabatarwa da Tattaunawa Kan Amfanin Sabbin Nau’ikan Dawa Masu Jure Sauyin Yanayi Domin Rage Talauci da Inganta Abinci a Najeriya.

 

Daga cikin manyan abokan aikin akwai Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS), Kungiyar Manoman Dawa da Masara ta Najeriya, da Tarayyar Turai (EU), da sauransu.

A jawabin sa, Mataimakin Daraktan NAERLS, Farfesa Muhammad Musa Jaliya, ya ce babban burin taron shi ne tabbatar da dorewar sabon tsarin nomar dawa a Najeriya.

 

“Ba ma so mu gudanar da aikin kawai ya ƙare ba tare da dorewa ba. Babban dalilin wannan taro shi ne samar da mafita don dorewar aikin. Manoma sun rungumi aikin, kuma sun samu sauyi ta fuskar iri na dawa masu inganci da fa’ida,” in ji shi.

 

A tattauna da Radio Nigeria Kaduna, Shugaban Kungiyar Manoman Dawa ta Kasa, Dr. Adamu Yusuf, ya jaddada muhimmancin Najeriya a matsayin jagora a noman dawa a duniya. Ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su ci gaba da addu’a da kokari domin kasar ta ci gaba da rike matsayinta a matsayin kasa ta daya ko ta biyu wajen noman dawa a duniya.

 

Ita ma a nata jawabin, Farfesa Aisha AbdulKadir daga IAR, ABU Zaria, ta bayyana cewa sun samu nasarar gabatar da sabbin nau’ikan iri na dawa a Najeriya.

 

“Muna son ganin mutane sun rungumi wadannan nau’ikan iri, muna kuma neman jin ra’ayoyin masu ruwa da tsaki da manoma don mu kara samun ci gaba,” in ji ta.

 

Wakilin ECOWAS a taron, Farfesa Mamman Saleh, ya bayyana cewa ECOWAS ta kuduri aniyar inganta rayuwar al’ummomin yankin ta hanyar bunkasa tattalin arziki da ayyukan noma.

“ECOWAS ta kafa hukumar kula da harkokin noma da albarkatun kasa domin tallafa wa ayyukan noman dawa na musamman, da nufin samar da ayyukan yi ga matasa da inganta gina kasa, da kuma dawo da filayen noma da suka lalace,” in ji shi.

 

Masu halarta taron sun fito ne daga Jihar Kaduna da sassa daban-daban da ke da alaka da harkar noman dawa.

 

Cov/Adamu Yusuf

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Dawa Najeriya

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga Sauyin Yanayi Da Lafiyarmu

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Tsawon lokaci, hukumomi a duniya suna gudanar da taruka don nemo hanyoyin daƙile ɗumamar yanayi kan irin illar da ke haifar wa rayuwar al’umma.

Ɗumama ko sauyin yanayi yana barazana ga duniya, yana haifar da sauye-sauye da masana ke cewa zai iya tsananta idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika Alƙawari NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan

Ɗaya daga cikin matsalolin da masana suka gano shi ne sare itatuwa ba tare da dasa sabbi ba, wanda ke illa ga muhalli.

Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazarin illar sare itatuwa ba tare da dasa wasu ba, da tasirinsa kan sauyin yanayi da kuma lafiyarmu.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Gargadi Gwamnatin Tarayya Kan Samar Da Karin Jami’o’i
  • An Yi Tarukan Tattaunawar Kasa Da Kasa Kan More Damammakin Sin A Havana Da Doha
  • NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga Sauyin Yanayi Da Lafiyarmu
  • Sin Ta Mika Tallafin Wasu Jirage Marasa Matuka Na Inganta Noma Ga Kasar Zambia
  • ’Yan adawa sun shirya ƙalubalantar Tinubu a zaɓen 2027 – Atiku
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika Alƙawari
  • An Gudanar Da Tarukan Tattaunawa Na Kasa Da Kasa Masu Jigon “Sin A Yanayin Bazara” A Turkiya Da Colombia
  • Wata Kungiya Mai Zaman Kanta Ta Samar Da Rijiyoyin Burtsatse A Karamar Hukumar Ringim
  • WSCIJ Ta Naɗa Farfesa Umaru Pate A Kwamitin Amintattu