Shugaban Kasar Iran Ya Bukaci Hadin Kai Tsakanin Iraniyawa Saboda Amfanin Kasar
Published: 21st, March 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan, a sakonsa na karshe ga Iraniyawa a shekara ta 1403 na kalandar Iraniyawa, ya bukaci mutanen kasar su hada kai don kaiwa ga manufofin kasar, wadanda suka hada da bunkasar tattalin arziki, da kauda tsadar rayuwa da kuma rashin bawa makiya damar cutar da kasar.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jawabinda na ‘Nuruz’ ko sabon shekara ta 1404 wanda ya shigo yau.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran, ta yi Tir da kwamatin tsaro kan rashin tabaka komai na takawa Amurka da Isra’ila birki
Iran ta yi Allah wadai da Kwamitin Sulhun na MDD na rashin tabaka komai wajen dakatar da ayyukan Amurka da Isra’ila wanda Iran din ta bayyana da abin kunya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi tir da munanan hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan kasar Yemen da kuma yadda gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da kai wa Falasdinawa hari a zirin Gaza, tare da yin Allah wadai da rashin daukar wami mataki daga kwamitin sulhu na fuskantar wadannan munanan ayyukan.
Esmaeil Baghaei, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana matukar na dama kan yadda ake kashe fararen hula da suka hada da mata da kananan yara da ba su ji ba ba su gani ba, da kuma lalata muhimman ababen more rayuwa na kasar Yemen, sakamakon hare-haren da Amurka ke kaiwa.
Ya bayyana hare-haren da Amurka ta kai ta sama a matsayin laifukan yaki da laifukan ta’addanci, yana mai danganta hakan da “abin kunya da rashin gaskiya” na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da sauran cibiyoyin kasa da kasa kan wannan ta’asa.
Ya ce Amurka da gwamnatin yahudawan sahyoniya sun kitsa wani shiri na hadin gwiwa na raunana al’ummar musulmi da kuma rufe duk wata muryar goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta.
Daga karshe Baghaei ya jaddada nauyin da ya rataya a wuyan kasashen musulmi na duniya na dakatar da zaluncin da Isra’ila ke yi da kuma hare-haren da sojojin Amurka suke yi a kan Falasdinawa da sauran al’ummar musulmi, yana mai kira ga gwamnatocin musulmi da su dauki matakin da ya dace da kuma kokarin da kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ke yi na shawo kan lamarin.
Akalla Falasdinawa 436 da suka hada da kananan yara 183 ne aka kashe tun bayan da Isra’ila ta keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza a ranar Talata.