Tinubu ya ba ni riƙon Ribas don wanzar da zaman lafiya — Ibas
Published: 21st, March 2025 GMT
Shugaban Riƙo na Jihar Ribas, Ibok Ibas, ya ce Shugaba Bola Tinubu, ya naɗa shi ne domin dawo da zaman lafiya a jihar, wadda ke fama da rikicin siyasa.
Da yake jawabi a wani shirin talabijin a daren Alhamis a Fatakwal, Ibas ya bayyana naɗin nasa a matsayin matakin da ya dace don kawo ƙarshen rikicin siyasa da ya ɗauki kusan shekaru biyu.
Ya ce rikicin ya hana ci gaban gwamnati, tare da haifar da matsalar tsaro da koma bayan tattalin arziƙi a jihar.
“A matsayina na ɗan yankin Neja Delta, na fahimci damuwar mutanenmu. Rashin tabbas a Jihar Ribas ya shafi iyalai, ’yan kasuwa da rayuwar yau da kullum.
“Naɗin da aka yi min ba na siyasa ba ne, sai dai don dawo da doka da oda, tare da tabbatar da cewa mutanenmu suna rayuwa cikin kwanciyar hankali.”
Ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa babban aikinsa shi ne dawo da zaman lafiya, tabbatar da bin doka da oda, tare da samar da yanayin da zai ba da damar ci gaban gwamnati da bunƙasa tattalin arziƙi.
“Ba aikin mutum ɗaya ba ne. Dole ne al’ummar Ribas su haɗa kai, dattawa, sarakunan gargajiya, ’yan siyasa, ’yan kasuwa, matasa da ƙungiyoyin fararen hula.
“Na zo a matsayin wanda zai hidimta wa jihar, wanda ke da nauyin dawo da zaman lafiya da tsari, domin Jihar Ribas ta dawo da matsayinta na cibiyar arziƙin man fetur a Najeriya.”
Ibas, ya gargaɗi ’yan jihar da su guji tashin hankali da aikata laifuka, inda ya bayyana cewa gwamnati ba za ta yarda da duk wani yunƙuri na kawo ruɗani ba.
Sai dai ya tabbatar da cewa zai mutunta haƙƙoƙin ’yan ƙasa tare da bin doka.
Ya buƙaci jama’a da su haɗa kai don girmama juna da samar da zaman lafiya a jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Naɗi Siyasa Zaman lafiya da zaman lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Iyaye Mata Sun Bukaci A Rika Samar Da Kayayyakin Bada Tazarar Haihuwa Akan Lokaci
Mata a Jihar Jigawa sun yi kira da gwamnati da kungiyoyin agaji masu zaman kansu da su samar da magungunan samun tazarar haihuwa kyauta domin inganta tsarin iyali.
Matan da suka tattauna da wakilinmu a cibiyoyin kula da lafiya na Kudai da Kachi dake Dutse, a yayin bikin ranar Lafiyar Uwa ta duniya, wato “Safe Motherhood” a turance, sun bayyana damuwarsu kan rashin samuwar kayayyakin bada tazarar haihuwa.
Wata uwa mai yara uku, Malama Karimatu Sani, ta ce duk lokacin da ta je siyan maganin samar da tazarar haihuwa, ana bata wadanda lokacin aikinsu ya wuce, wanda hakan na iya haifar da illa ga lafiyar mata.
“Sau da dama sai na jira asibiti ya samu sababbin kaya, ina addu’ar kada na samu ciki kafin a kawo wadannan magunguna da ake badawa kyauta.” in ji ta.
Wata mai suna Maryam Abubakar, ta bayyana cewa tana kashe kudi masu yawa wajen zuwa asibiti don dubawa ko kayan sun samu.
Ta koka da cewa siyan kayan bada tazarar haihuwa daga shagunan magani a waje yana da tsada sosai wanda hakan yana hana mata damar siya.
A madadin mata na jihar, ta yi kira ga gwamnati da kungiyoyin agaji da su kawo musu dauki domin mutane da dama suna rungumar tsarin tsara iyali a matsayin mafita ga matsalolin da ke damun al’umma.
A gefe guda, wata ma’aikaciyar lafiya a cibiyar kula da lafiya ta Kachi, Amina Sulaiman, ta tabbatar da cewa kayayyakin samar da tazarar haihuwa sun kare a asibitin tun watanni biyu da suka wuce.
“Muna takaicin yadda mata sukan zo don yin tsarin iyali amma babu biyan bukata saboda rashin kayan aiki da magunguna”.
Hajiya Amina Sulaiman ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da ssusamar da kayayyakin don ragewa mata radadin rayuwa.
A bara ne gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da kwamiti mai mambobi ashirin da uku kan Lafiyar Uwa, da ke da alhakin farfado da hanyoyin kula da lafiyar uwa a jihar.
Sakataren gwamnatin jihar, Malam Bala Ibrahim, yayin kaddamar da kwamitin a ofishinsa, ya bayyana cewa aikin kwamitin ya hada da duba yadda ake aiwatar da shirin Lafiyar Uwa da kirkirar tsarin aiwatarwa domin karfafa abinci mai gina jiki da shawarwari don samun kulawa da uwa da jarirai.
Sauran ayyukan sun hada da yin bincike kan yadda shirin ke gudana da kirkirar hanyoyi don karfafa tura mata zuwa cibiyoyin lafiya daga cikin al’umma.
Yayin kaddamar da kwamitin, Malam Bala Ibrahim ya kara da cewa an fara aiwatar da shirin ne a shekarar 2006 karkashin shirin tallafin na DFID.
Ya ce daya daga cikin muhimman sassa na shirin shi ne tsarin daukar gaggawa, inda aka samar da motoci don daukar mata masu nakuda zuwa cibiyar lafiya mafi kusa don samun ingantacciyar kulawa.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, maza da mata da dama daga yankunan karkara a jihar Jigawa sun rungumi tsarin bada tazarar haihuwa da shirin Lafiyar Uwa, suna kuma cin moriyar su ta bangaren lafiya da tattalin arziki.
Usman Mohammed Zaria