Leadership News Hausa:
2025-03-21@19:29:14 GMT

Majalisar Dokokin Nijeriya Ta Zama Ƴar Amshin Shata — Kwankwaso

Published: 21st, March 2025 GMT

Majalisar Dokokin Nijeriya Ta Zama Ƴar Amshin Shata — Kwankwaso

Jagoran jam’iyyar adawa ta NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki Majalisar dokoki ta 10 a Nijeriya bisa amincewarta da ƙaddamar da dokar ta ɓaci (State of Emergency) a Jihar Ribas da kuma dakatar da gwamnan jihar da  mataimakinsa da majalisar dokokin jihar daga aiki ta hanyar shugaban ƙasa Bola Tinubu, yana mai cewa ‘yan majalisar sun zama kamar ƴan amshin Shata.

Kwankwaso, wanda ya riƙe muƙamin gwamnan jihar Kano sau biyu, ya ga baiken wannan mataki na majalisar, in da ya ce yayi kama da irin kuskuren da ‘yan majalisar tarayya suka yi a lokacin majalisa ta uku (Third Republic), wanda ya haifar da soke zaɓensu na ranar 12 ga Yuni, 1993. Ya bayyana cewa ƴan majalisar ya kamata ta juya wa wannan rashin adalci da shugaban ƙasa Tinubu ya aikata a Rivers, amma sun sai suka zaɓi goyon bayan wannan mataki wanda yake ba bisa ƙa’ida ba.

Ba Na Goyon Bayan Dakatar Da Gwamnan Jihar Ribas – Ndume Jigon APC Ya Fara Yunkurin Sulhunta Kwankwaso, Ganduje Da Shekarau

Kwankwaso ya ci gaba da cewa wannan matakin da shugaban ƙasa Tinubu ya ɗauka na dakatar da dukkan jami’an da suke zaɓaɓɓu a jihar Ribas ya saɓa wa kundin tsarin mulki, yana kuma kawo barazana ga tsarin dimokuraɗiyya. Ya bayyana damuwarsa game da yadda majalisar ta yi amfani da tsarin zabe na muryar wajen goyon baya (voice vote) wanda bai dace da ƙa’idojin zaɓe na ƙasa ba.

Kwankwaso ya ƙara da cewa wannan mataki na iya kawo matsala ga ci gaban dimokuraɗiyyar da aka samu cikin shekaru 26 na dawowarta.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Kwankwaso

এছাড়াও পড়ুন:

Kotun Ta Dakatar Da INEC Karɓar Buƙatar Yin Kiranye Ga Senata Natasha

Kotun Tarayya da ke Lokoja, Jihar Kogi, ta bayar da umarnin dakatar da Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC) daga karɓar kowace buƙatar da aka gabatar domin fara shirin kiranye ga Senata Natasha Akpoti-Uduaghan daga Majalisar Dattawa.

Haka kuma, kotun ta hana ma’aikatan INEC, da wakilansu, ko duk wani wanda ke da hannu daga karɓar ko yin aiki da kowace buƙata da ke ɗauke da sunayen ƙarya daga mutanen mazaɓar Kogi ta tsakiya, sannan ta hana gudanar da kowanne zaɓe ko taro kan lamarin har sai kotu ta yanke hukunci.

Kwamitin Majalisa Ya Yi Watsi Da Ƙorafin Da Natasha Ta Shigar A Kan Akpabio Majalisar Dattawa Ta Dakatar Da Sanata Natasha Na tsawon Watanni 6 Saboda Rashin Da’a

An bayar da wannan umarnin ne bayan buƙatar gaggawa da Anebe Jacob Ogirima da wasu mutane huɗu daga yankin Kogi ta tsakiya, waɗanda suka yi rajista a matsayin masu zabe suka yi. Buƙatar ta samu wakilcin lauya Smart Nwachimere, na West-Idahosa, SAN & Co., inda kotu ta ɗage shari’ar zuwa 6 ga Mayu, 2025, don samun rahoton aikawa da gayyata da kuma ci gaba da sauraron shari’ar.

A cikin martani ga wannan hukunci, wata ƙungiya mai suna, Action Collective, ta yabawa kotu bisa wannan umarnin, inda shugaban ƙungiyar, Dr. Onimisi Ibrahim, ya ce wannan umarnin zai ƙara bayyana rashin biyayya daga wasu mutanen da ke goyon bayan shirin ƙoƙarin cire Natasha daga Majalisar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kotun Ta Dakatar Da INEC Karɓar Buƙatar Yin Kiranye Ga Senata Natasha
  • Kwankwaso ya yi Allah-wadai da ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas
  • Tinubu Ya Yaba Wa Majalisar Dokoki Kan Amincewa Da Dokar Ta-Ɓaci A Jihar Ribas
  • Mun Yi Watsi Da Ayyana Dokar Ta-Ɓaci Da Tinubu Ya Yi A Ribas – Shugabannin Adawa
  • Majalisar wakilai ta amince da dokar ta-ɓaci a Ribas
  • Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas
  • Atiku Ya Soki Tinubu Kan Ayyana Dokar Ta-ɓaci a Jihar Ribas
  • Waiwaye: Jihohin Da Aka Taɓa Sanya Dokar Ta-ɓaci A Nijeriya
  • Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Gwamnan Jihar Rivers Da ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar