Kotun Tarayya da ke Lokoja, Jihar Kogi, ta bayar da umarnin dakatar da Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC) daga karɓar kowace buƙatar da aka gabatar domin fara shirin kiranye ga Senata Natasha Akpoti-Uduaghan daga Majalisar Dattawa.

Haka kuma, kotun ta hana ma’aikatan INEC, da wakilansu, ko duk wani wanda ke da hannu daga karɓar ko yin aiki da kowace buƙata da ke ɗauke da sunayen ƙarya daga mutanen mazaɓar Kogi ta tsakiya, sannan ta hana gudanar da kowanne zaɓe ko taro kan lamarin har sai kotu ta yanke hukunci.

Kwamitin Majalisa Ya Yi Watsi Da Ƙorafin Da Natasha Ta Shigar A Kan Akpabio Majalisar Dattawa Ta Dakatar Da Sanata Natasha Na tsawon Watanni 6 Saboda Rashin Da’a

An bayar da wannan umarnin ne bayan buƙatar gaggawa da Anebe Jacob Ogirima da wasu mutane huɗu daga yankin Kogi ta tsakiya, waɗanda suka yi rajista a matsayin masu zabe suka yi. Buƙatar ta samu wakilcin lauya Smart Nwachimere, na West-Idahosa, SAN & Co., inda kotu ta ɗage shari’ar zuwa 6 ga Mayu, 2025, don samun rahoton aikawa da gayyata da kuma ci gaba da sauraron shari’ar.

A cikin martani ga wannan hukunci, wata ƙungiya mai suna, Action Collective, ta yabawa kotu bisa wannan umarnin, inda shugaban ƙungiyar, Dr. Onimisi Ibrahim, ya ce wannan umarnin zai ƙara bayyana rashin biyayya daga wasu mutanen da ke goyon bayan shirin ƙoƙarin cire Natasha daga Majalisar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a Naira

Matatar Dangote ta sanar da dakatar da sayar da Man Fetur da Naira na wucin gadi.

Kamfanin ya bayyana wannan mataki ne a cikin wata sanarwa da ya aike wa dillalan man fetur a ranar Laraba da rana.

Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya fice daga gidan gwamnatin Ribas  Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas

A cewar sanarwar, matatar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin guje wa matsalar biyan kuɗin ɗanyen mai da ta ke saya da dalar Amurka.

“Ya zuwa yanzu, mun sayar da sama da adadin man fetur da muka samu a Naira.

“Domin daidaita cinikayyarmu da sayen ɗanyen mai, dole ne mu ɗauki wannan mataki na wucin gadi,” in ji sanarwar.

Kamfanin Dangote ya kuma ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ya dakatar da sayar.

Kamfanin ya ce wannan labari ba gaskiya ba ne, inda ya jaddada cewa tsarinsa yana da inganci kuma ba a samu wata matsala ba.

Matatar ta Dangote ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sayar da mai a Naira da zarar ta samu ɗanyen mai da aka sayar mata a Naira daga kamfanin NNPC.

“Muna nan daram wajen yi wa kasuwar Najeriya hidima, kuma za mu dawo da sayar da mai a Naira da zarar mun samu kaya,” in ji sanarwar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kotun Ta Dakatar Da INEC Karɓar Buƙatar Yin Kiranye Ga Senata Natasha
  • Wata Kotu A Abuja Ta Kori Karar Da Karuwai Suka Shigar Gabanta
  • Majalisar Dokokin Nijeriya Ta Zama Ƴar Amshin Shata — Kwankwaso
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [12]
  • Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a Naira
  • Ribas: Fubara Ya Fice Daga Gidan Gwamnati Yayin Da Sabon Shugaba Ke Shirin Karɓar Mulki
  • ’Yan Banga Sun Ceto Mutum 3 Daga Hannun ’Yan Bindiga A Taraba
  • DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen Gwamna
  • Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Gwamnan Jihar Rivers Da ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar