Sojoji sun ceto mutum 84 da ’yan bindiga suka sace a Katsina
Published: 21st, March 2025 GMT
Dakarun Sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 84 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Kankara a Jihar Katsina.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Nasir Mu’azu, ya bayyana cewa sojojin runduna ta 17 tare da tallafin jiragen yaƙi sun kai farmaki maɓoyar ’yan ta’adda da ke yankin Sanusi Dutsin-Ma da tsaunukan Pauwa.
Ya ce a yayin farmakin dakarun sun kashe wasu daga cikin ’yan bindiga sannan suka kuɓutar da waɗanda aka sace.
Daga cikin mutanen da aka ceto, akwai maza bakwai, mata 23, da yara 54.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta yaba wa sojojin bisa ƙoƙarinsu, kuma tuni aka samar da abinci da kulawa ga mutanen da aka kuɓutar, kafin a mayar da su ga iyalansu.
Ya ƙara da cewa Gwamnatin Katsina ba za ta yi sulhu da ’yan ta’adda ba, domin tana da niyyar ci gaba da yaƙi da su har sai an daƙile matsalar garkuwa da mutane a jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga dakaru Garkuwa Kwamishina yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
An shiga zaman ɗar-ɗar yayin da sojoji suka mamaye Gidan Gwamnatin Ribas
Mazauna sun shiga zaman ɗar-ɗar a yayin da motocin yaƙi na sojoji suka mamaye Gidan Gwamnatin Jihar Ribas.
Wannan dai na zuwa ne jim kaɗan bayan Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar.
Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau Tinubu ya sanya dokar ta-baci a Jihar RibasWata majiya ta shaida wa Aminiya cewa fiye da motocin soji 10 aka hanga suna sintiri a kan hanyar zuwa gidan gwamnatin yayin da wasu motocin yaƙi masu sulke suka tsaya wuri-wuri a hanyar.
Majiyar ta ce titunan birnin na Fatakwal sun zama fayau a yayin da mazauna suka tsere gidajensu.
Babu tabbaci ko gwamnan da aka dakatar, Similanayi Fubara yana cikin gidan gwamnatin a halin yanzu.
Sai dai majiyoyi sun ce akwai yiwuwar gwamnan ya samu labarin cewa za a ayyana dokar ta ɓacin tun kafin faruwar lamarin.
Bayanai sun ce gwamnan ya shafe tsawon wunin wannan rana ta Talata yana ganawa da ’yan majalisar zartarwarsa.
A halin yanzu dai birnin na Fatakwal ya zama fayau a yayin mazauna da ’yan kasuwa duk sun koma gidajensu.
Dalilin da Tinubu ya ayyana dokar ta ɓacinTinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas bayan rikita-rikitar siyasa da jihar ta daɗe tana fama da shi tare da kuma da naɗa wanda zai riƙe muƙamin gwamnan jihar na tsawon wata shida.
Tinubu ya sanar da matakin ne a wani jawabi da ya yi ta kafafen talabijin na ƙasar da yammacin ranar Talata.
A cikin jawabin nasa, Tinubu ya yi nuni da yadda aka rushe ginin majalisar dokokin jihar watanni 18 da suka gabata, wadda aka kasa sake gina ta har zuwa wannan lokaci.
“Jihar ta tsaya cik tun bayan ɓarkewar rikicin siyasar inda aka tauye wa al’ummar jihar hakkinsu na cin moriyar mulkin dimokuraɗiyya.
“Na yi iyakar bakin ƙoƙarina wajen ganin yadda za a magance matsalar to amma duka ɓangarorin sun yi watsi da yunkurin.
“Bayan nazari kan halin da ake ciki a jihar Rivers, ya zama wajibi na yi amfani da sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.
“A kan haka, na ayyana dokar ta-ɓaci daga yau 18 ga watan Maris, 2025.
“Da wannan bayani, gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Mrs Ngozi Odu da kuma dukkanin zaɓaɓbun ƴanmajalisar dokokin Jihar Ribas, an dakatar da su na wata shida, a matakin farko.
“A halin yanzu, na naɗa Vice Admiral Ibokette Ibas a matsayin wanda zai gudanar da lamurran jihar, domin amfanin al’ummar jihar,” in ji Tinubu.
Sai dai a cikin jawabin nasa, Tinubu ya bayyana cewa wannan doka da ya ƙaƙaba ba ta shafi ɓangaren shari’a na jihar ba.