An Yi Tarukan Tattaunawar Kasa Da Kasa Kan More Damammakin Sin A Havana Da Doha
Published: 21st, March 2025 GMT
An yi taron tattaunawar kasa da kasa mai taken “Sin a lokacin bazara: More damammakin da take samarwa a duniya” a birnin Havana dake kasar Cuba, a ranar 19 ga wannan wata, inda shugaban CMG Shen Haixiong da jakadan Sin dake kasar Cuba Hua Xin suka gabatar da jawabi. Mahalarta taron fiye da dari sun tattauna kan damammakin da tsarin zamanantar da al’ummar Sinawa na Sin ke samar wa kasar Cuba da yankin Latin Amurka.
Har ila yau, duk dai a wannan ranar, an yi taron tattaunawar a birnin Doha dake kasar Qatar, inda shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. Kana, mahalartar taron sun tattauna kan samun bunkasa mai inganci da damammakin da Sin ta samar wa kasar Qatar a karkashin manufar bude kofa ga kasashen waje da dai sauransu. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An Kaddamar Da Bikin Nuna Fina-Finan Sinanci Na CMG Karo Na 5
Yau Alhamis ranar 10 ga wata, an fara “Ranar Sinanci ta MDD” ta shekarar 2025, wato bikin nuna fina-finan Sinanci na babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin na CMG karo na 5 a hukumance.
An kaddamar da bikin bisa hadin gwiwar CMG da kungiyar wakilan kasar Sin na MDD dake birnin Geneva da na sauran kungiyoyin kasa da kasa, da ofishin MDD dake birnin Geneva. Daga cikin shirye-shiryen bikin mai taken “Ziyara A kasar Sin” wato “China Travel” a Turance, an gayyaci jama’ar kasashen duniya da su tsara bidiyo game da ziyararsu a kasar Sin, inda suka nuna kyawawan al’adu da zamantakewar al’umma na kasar Sin, da kuma yanayin bunkasuwar kasa, domin samar wa al’ummomin damar kara fahimtarsu game da kasar Sin. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp