Taƙaddama: An kama wanda ya daɓa wa matarsa wuƙa ta mutu
Published: 21st, March 2025 GMT
Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas ta sanar da kama Mista Peter Dike da ake zargi da kashe matarsa a gidansu da ke Unguwar Oke-Ira Ilogbo Eremi, Marogbo.
Rundunar ’yan sandan a ranar Alhamis ta bayyana cewa wanda ake zargin ya daɓa wa matarsa wuƙa har lahira a lokacin da suka yi ƙazamin faɗa da ya ɓarke a gidan nasu sanadin taƙaddama a ranar Laraba.
Wannan mummunan al’amari ya ƙara dagula al’amuran tashin hankali a cikin gidan ma’aratan da ya kawo sanadin mutuwar matar aure.
A watan Oktoban 2024, an kuma kama Motunrayo Olaniyi da laifin daɓa wa amaryarsa, Olajumoke wuƙa har lahira, a yayin wata hatsaniya mai zafi a gidan su a rukunin gidaje na Amazing Grace Estate, Elepe, a yankin Ikorodu.
Da yake ƙarin haske kan lamarin a ranar Laraba, jami’in hulɗa da jama’a na ’yan sandan, CSP Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa an sanar da jami’an tsaro na sashen Morogbo, kuma ba tare da ɓata lokaci ba suka isa wurin.
Hundeyin ya ci gaba da cewa, “An tabbatar da al’amarin, bayan da jami’an ‘yan sanda da ke sintiri a cikin garin da ke yankin suka samu labarin, sai suka shiga cikin gaggawa suka cafke wanda ake zargin, an samu wuƙar kicin guda ɗaya da tabo da jini daga wajensa, aka kawo shi ofishin aka yi masa tambayoyi.
“Ya amsa laifinsa, an ajiye gawar a ɗakin ajiyar gawa na babban asibitin Badagry, kuma za a miƙa ƙarar zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar, Panti Yaba.”
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano
’Yan sanda sun cafke wasu mutum takwas da ake zargi da faɗan daba a yankin Ƙofar Na’isa zuwa Ƙofar Ɗan Agundi da ke ƙwaryar birnin Kano.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ziyarar da Atiku ya kai wa Buhari ba ta dami APC ba — Ganduje Yadda bom ya tashi da ɗan gwangwan a LegasKiyawa ya ce a ranar Alhamis da ta gabata ce suka samu kiraye-kirayen waya cewa wasu sun fito da makamai suna faɗan daba, lamarin da ya sanya aka tura jami’ai domin ɗaukar mataki.
Kakakin ’yan sandan ya ce a wannan lokaci babu wanda aka kama sakamakon arcewa da masu faɗan daban suka yi.
“Wasu sun fito faɗan daba, sun ji wa kansu raunuka a Ƙofar Na’isa, amma ba wanda ya zo wajen ’yan sanda a kai shi asibiti,” a cewar Kiyawa.
Sai dai Kiyawa ya ƙara da cewa jami’ansu sun sake komawa unguwar da daddare, inda suka cafke mutum takwas da raunuka a jikinsu da wuƙaƙe.
Kazalika, ya ce sun tattara sunayen mutane daban-daban da ake zarginsu da faɗace-faɗacen daba kuma nan ba da jimawa ba za su shiga hannu.
Aminiya ta rawaito yadda ake zaman ɗar-ɗar a yankin Ƙofar Na’isa da kuma Ƙofar Ɗan Agundi tun bayan dawowar faɗan daban a yayin bukukuwan sallah ƙarama da aka yi kwanan nan.