Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; Amurkawa su kwana da sanin cewa, babu wani abu da za su samu, ta hanyar yi wa Iran barazana, kuma waninsu ma ya sani cewa, idan har su ka aikata wani abu maras  kyau akan Iran, to za su fuskanci mayar da martani mai tsanani.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi a yau Juma’a dangane da bikin sabuwar shekara ta Noruz a Husainiyyar Imam Khumaini dake nan Tehran, ya bayyana cewa; Babban kusakuren ‘yan siyasar Amurka da kuma na  Turai , shi ne daukar ‘yan gwagwarmaya a wannan yankin da cewa  ‘yan koren Iran, da hakan batunci a gare su.”

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kara da cewa;  Al’ummar Yemen, kamar sauran ‘yan gwgawarmaya a cikin wannan yankin suna da dalilai na gwgawarmaya, Iran kuwa ba ta da bukatar ‘yan kore.”

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma kara da cewa; “Ko kadan, ba mu ne farau ba acikin wannan rikicin,amma idan wani ya fara aikata wani abu mummuna, to zai fuskanci  mayar da martani mai tsanani.

Jagoran juyin musuluncin ya kuma ce; Karshen abinda zai faru da gwgawarmaya shi ne cin kasar abokan gaba ‘yan  sahayonoya.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma ce; Abinda ‘yan sahayoniya marasa rahama suke yi,ya sosa zukatan al’ummu musulmi da wadanda ba musulmi ba.

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya yi bitar muhimman abubuwan da su ka faru a shekarar da ta gabata ta hijira shamshiyya da su ka hada mai daci da kuma dadi. Daga ciki ya bayyana hatsarin da faru a wurin hako ma’adanai na Tabas, dake arewacin Iran, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 50.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Jagoran juyin

এছাড়াও পড়ুন:

Wata Kungiya Mai Zaman Kanta Ta Samar Da Rijiyoyin Burtsatse A Karamar Hukumar Ringim

Wata Kungiyar Agaji Mai Zaman Kanta, Ike Odoeme Foundation, ta taimaka wa yankuna biyu a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa, ta hanyar haka rijiyoyin burtsatse guda bibbiyu a kowane yanki.

A yayin kaddamar da ayyukan a kauyukan Facawa da Riniyal da ke  Ringim, jami’ar shirye-shirye ta gidauniyar, Miss Suzie Agas, ta bayyana jin dadinsu na yin tasiri a rayuwar al’ummar yankin.

 

A cewarta, wannan aikin yana tabbatar da kudirin gidauniyar na tabbatar da cewa kowace al’umma tana da damar samun tsaftataccen ruwa, ba tare da la’akari da matsayinta ko inda take ba.

Suzie Agas ta jaddada cewa ruwa yana da matukar muhimmanci ga kiwon lafiya da ci gaban tattalin arziki, amma abin takaici, al’ummomi da dama na fuskantar kalubale wajen samun tsaftataccen ruwa.

Ta kara da cewa rashin ruwa mai tsafta yana haddasa cututtukan da ake dauka ta ruwa, yana hana mutane yin ayyuka da kyau, kuma yana rage damarmakin yaran makaranta don mayar da hankali kan karatunsu.

Suzie ta gode wa hukumomin karamar hukumar Ringim bisa goyon baya da hadin kai da suka bayar wajen tabbatar da tsaro da aminci a lokacin aikin.

Ta kuma roki al’ummomin Facawa da Riniyal da su kula da rijiyoyin, don gujewa samun matsala.

A nasa jawabin yayin kaddamar da rijiyoyin, hakimin Sankara, Alhaji Yusi Ahmed, ya tabbatar da cewa wadannan al’ummomi sun shafe shekaru da dama suna fama da karancin ruwa.

Ya ce ko da yake an taba samar da rijiyoyi a wadannan yankuna, rashin kulawa da su ya sa suka lalace.

Ya bukaci mazauna yankin da su dauki nauyin kula da rijiyoyin domin su dade suna amfani da su fiye da wadanda aka samar a baya.

Shi ma da yake nasa jawabi, Shugaban Karamar Hukumar Ringim, Alhaji Badamasi Dabi, ya jinjinawa gidauniyar bisa jajircewarta wajen tabbatar da kammala aikin.

Ya bayyana cewa karamar hukumar Ringim tana da cikakken shirin yin hadin gwiwa da kungiyoyin agaji domin ci gaban al’umma.

Bayan haka, gidauniyar ta rabawa al’ummar buhunan shinkafa.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana godiyarsu bisa wannan aikin, inda suka ce hakan ya rage wahalar da ‘ya’yansu ke fuskanta wajen yin doguwar tafiya domin samo ruwa.

 

Usman Muhammad Zaria 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araghchi : Iran za ta mayar da amsa ga wasikar Trump cikin kwanaki masu zuwa
  • Iran, ta yi Tir da kwamatin tsaro kan rashin tabaka komai na takawa Amurka da Isra’ila birki
  • MAGGI: Girke-girken Ramadan masu kawo sauyi da zumunta
  • Iran: Jagora ya yi kira da a karfafa dogaro da kai a cikin gida domin dakile tasirin takunkumai
  • Jakadan Amurka Ya Ziyarci Sarkin Zazzau Domin Karfafa Alakar Amurka Da Najeriya
  • Trump, ya ce ya yi tattauna mai armashi da Zelensky, bayan wacce ya yi da Putin
  • Wata Kungiya Mai Zaman Kanta Ta Samar Da Rijiyoyin Burtsatse A Karamar Hukumar Ringim
  • Amurka ce Kadai Ta Ki Yin Allawadai Da Killace Gaza A Tsakanin Mambobin Kwamitin Tsaro na MDD
  • HOTUNA: An yi gobara a kasuwar ’yan gwan-gwan da ke Kano