Cibiya Mai Fafutukar Kare Hakkokin Falasdinawa “Global 195” Ta Shelanta Farautar Sojojin HKI Da Su KaTafka Laifukan Yaki
Published: 21st, March 2025 GMT
Cibiyar ta “ Global 196” ta bakin babban shugabanta ta sanar da cewa a cikin watanni 18 da su ka gabata, ta tattara bayanai akan laifukan yakin da Isra’ila ta tafka a Gaza.” Haka nan kuma cibiyar mai matsuguni a Birtaniya ta ce, ya zuwa yanzu ta tattara da dalilai da su ka dace da ka’idojin shari’a a kotunan manyan laifuka na kasar.
Har ila yau cibiyar ta ce, bayan kammala tattara bayanai a zango na farko, za kuma ta bude shafi na gaba domin kara samun wasu bayanan da za su tabbatar da cewa an yi wa Isra’ilawan hukunci a cikin kasashen duniya, musamman masu dauke da zama ‘yan kasashe biyu.
Wani shiri da wannan cibiyar take da shi,shi ne na samar da wasu cibiyoyin a cikin nahiyoyin duniya da samar da ka’idoji ta fuskar shari’a da su ka dace da na duniya da kuma na kasashe domin farautar wadanda su ka aikata laifukan yaki a Gaza, da fitar da sammacin kamo su, saboda su fuskanci shari’a.
Wadanda wannan cibiyar take son ganin sun fuskanci shiri’a, sun hada jami’an sojan HKI, da ‘yan siyasa da duk masu hannu a aikata laifukan yaki.
Ita wannan cibiyar ta kunshi kawance na lauyoyi daga kasashen Malysia, Turkiya, Norway, Canada, Bosnia, da kuma Birtaniya.
Ana kuma sa ran cewa anan gaba wasu lauyoyin daga wasu kasashen duniya za su shiga ciki,musamman a wannan lokacin da HKI ta bude wani sabon kisan kiyashin akan al’ummar Falasdinu.
Cibiyar ta kasa da kasa mai son ganin an yi wa Falasdinawa adalci, ta kuma hada da fitaccen lauyan nan dan kasar Afirka Ta Kudu John Dugard, da kokarin jawo lauyoyi daga dukkakin kasashen duniya.
Cibiyar za ta yi aiki domin ganin a kowace jaha da gunduma ta kasashen duniya an samar da hanyar hukunta wadanda su ka aikata laifukan yaki a Gaza.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasashen duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Kare-Karen Haraji Ba Zai Bunkasa Arzikin Amurka Ba
Bugu da kari, masharhanta da dama na ganin karin harajin fito ba zai warware matsalar da Amurkan ke ciki ba. Ko shakka babu idan Amurka na son ta tunkari wannan kalubale bisa gaskiya, sai ta sauya tsarin ilimi, ta kuma bunkasa fannin kirkire-kirkirenta, da daga martabar masana’antu, da zuba jari na dogon lokaci a fannin, ba wai matakin jeka-na-yika na gajeren lokaci, irin wannan na baiwa kasuwa kariyar cinikayya ba.
A daya hannun kuma baya ga illar da wannan kare-karen haraji ya haifar, matakan kasashen da lamarin ya shafa na ramuwar gayya na iya haifar da hauhawar farashi na gaggawa, da jefa tattalin arzikin sassa daban daban cikin halin komada, a maimakon fatan da gwamnatin Amurkan ke yi na sake mayar da kasar “Zakaran gwajin dafi.” (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp