Sojojin Sudan Sun Kwace Iko Da Fadar Shugaban Kasa A Birnin Khartum
Published: 21st, March 2025 GMT
Sojojin Sudan sun sanar a yau Juma’a cewa sun kwace iko da fadar shugaban kasa dake tsakiyar birnin Khartum, bayan da su ka kori mayakan rundunar kai daukin gaggawa.
Majiyar ta ce, sojojin na Sudan sun fara da kutsawa cikin fadar shugaban kasar ne, ta mashigar gabas,bayan da su ka kashe mayakan rundunar kai daukin gaggawa da dama,yayin da wasu da dama su ka gudu zuwa cikin kasuwar dake kusa.
Bayanin da sojojin na Sudan su ka fitar ya kunshi cewa; Mun murkushe mayakan Duqlu, ‘yan ta’adda a tsakiyar birnin Khartum da kuma kasuwar Larabawa da ginin fadar shugaban kasa da sauran ma’aikatu.”
Har ila yau majiyar sojan na Sudan ta ce,su kuma yi nasarar rusa makamai da motocin yakin rundunar kai daukin ggagawar,kamar kuma yadda ta kame wasu masu maya.
Janar Nabil Abdullah wanda shi ne kakakin sojan na Sudan ya sanar da cewa; Za su ci gaba kai hare-hare a cikin dukkanin fagagen yaki har samun nasara.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Brice Ologui Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Gaban Da Kashi 90.35% A Jiya Lahadi
Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Gabon wanda kuma ya jagoranci juyin mulkin da aka yiwa Ali Bongo tsahon shugaban kasar ya lashe zaben da aka gudanar a jiya Lahadi tsakanin yan takara 7 har da shi.
Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News” ya bayyana cewa Oligui dan shekara 50 a duniya, shi ne babban dogarin sojoji masu tsare fadar shugaban kasar Gaban, a lokacinda ya jagoranci juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin da yan gidan Bogo suka yi na shekaru kimani 50 a kasar.
Labarin ya kara da cewa kashi 2/3 na mutanen Gabon wadanda yawansu bai fi miliyon 2.3 ba suna cikin talauci a cikin kasa wacce take da arziki mai yawa.
Brice zai jagoranci kasar na tsawon shekaru 7 masu zuwa kuma yana iya sake shi takarar shugabancin kasa karo na biyu.
Yan takara 6 ne suka tsaya tare da Brice amma mai binsa bai sami fiye da kashi 3 % na kuri’un da aka kada ba sannan yawan fitowar mutane masu zabe ya kai kashi 70.4% wanda ya nuna cewa an sami sauyi babban a cikin harkokin siyasar kasar ta Gabaon.