Masu Ruwa Da Tsaki Sun Gargadi Gwamnatin Tarayya Kan Samar Da Karin Jami’o’i
Published: 21st, March 2025 GMT
Sun kuma bayyana cewa, wajibi ne gwamnati ta mayar da hankali wajen inganta manyan makarantun da ake da su na tarayya da kuma jihohi, ta hanyar samar da wadatattun kudade, inganta abubuwan more rayuwa da kuma tabbatar da ganin ma’aikatan jami’i’on, sun samu horo na musamman da suke bukata da kuma tallafa musu.
Wani mai ba da shawara a kan harkokin binciken ilimi a Jami’ar Abuja, Humphrey Ukeaja, ya gano wasu damammaki da kalubale iri-iri da aka samu kwanan nan.
Masanin ya yi nuni da cewa, rashin samun wadatattun kudade a fannin ilimi a Nijeriya, ya zama wani babban al’amari. “Idan kuna son yin wannan sauyi misali, mayar da jami’i’o’i zuwa na gwamnatin tarayya, har yanzu a kwai ayar tambaya, shin za ku inganta su ne kokuwa inganta kudaden da za a bai wa sabbin jami’o’in? Domin kuwa, wannan ba karamin kalubale ba ne. saboda haka, gwamnati tana da kyakkyawan kudiri ne na daukar cikakken nauyin wannan ilimi?”.
Canzawa tare da kara wasu makarantu ba tare da daukar cikakken nauyinsu ba, zai sa ba za su iya tsayawa da kafafunsa, wanda a karshe ko kadan ba za a samu abin da ake nema ba na biyan bukata, in ji shi.
Farfesa Ukeaja, na da ra’ayin cewa, kafa jami’o’in tarayya a wurare kamar Kachia, zai taimaka wajen inganta ilimi tare da rage tazarar da ke tsakanin birane da kauyuka ta fannin samar da ilimi. “Don haka, idan har za a samar da jami’o’i a wuraren da suka dace, babu shakka wannan zai zama wani babban ci gaba”, in ji shi.
Ya ba da shawarar cewa, ya kamata gwamnatin tarayya ta kara yawan kudade ga fannin ilimi tare da fadada hadin gwiwa da jami’o’i masu zaman kansu, domin inganta jami’o’in, bai wa malamai horo na musamman da sauran makamantansu.
Har ila yau, kungiyar daliban Nijeriya; sun yaba da matakin, amma kuma sun nuna damuwa a kan lamarin.
Jami’in hulda da jama’a na kungiyar dalibai ta kasa (NANS), Kwamared Samson Ajasa Adeyemi, ya bayyana jin dadinsa kan kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na magance matsalolin ilimi a Nijeriya, musamman kan yadda take mayar da makarantun jihohi zuwa na tarayya.
Sai dai ya koka da cewa, daya daga cikin manyan kalubalen da ke fuskantar fannin na ilimi a Nijeriya, ya hada da rashin isasssun kudade.
Ajasa ya yi nuni da cewa, da dama daga cikin wadannan manyan makarantun gwamnati, sun dogara ne da kudaden basussuka wajen tafiyar da makarantun, sannan akwai bukatar aiwatar da gaskiya wajen aiwatar da kasafin kudin yadda ya kamata, domin tabbatar da ganin an yi amfani da wadannan kudade yadda ya dace.
A nasa bangaren, wani dan kishin kasa, Mista Tochukwu Osuagwu, ya bukaci gwamnati ta kara zuba hannun jari a jami’o’in da ake da su, domin inganta su yadda ya kamata.
“Me zai hana a mayar da hankali wajen inganta jami’o’in da ake da su a fadin wannan kasa baki-daya, ko shakka babu, Nijeriya za ta ci gaba idan muka riki junanmu da gaskiya.
“A bayyane yake cewa, jami’o’inmu na cikin wani mummunan yanayi, wanda ba haka ya kamata al’amarin ya kasance ba, kyautuwa ya yi a ce jami’o’inmu sun samu wadatattun kayan aiki da ci gaba kamar yadda ake gani a wasu sauran kasashe”, in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Mutum ɗaya ya mutu a faɗan ƙungiyar asiri a Maiduguri
Wani matashi ɗan shekara 18 mai suna Bakura Muhammed, ya gamu da ajalinsa a wani rikici da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin matasa masu gaba da juna da ake wa laƙabi da Malians a Maiduguri.
Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zaga-zola Makama cewa, rikicin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar 4 ga watan Afrilun nan a yankin Ajari da Tashar Lara, inda matasan ɓangarorin biyu suka yi artabu da juna.
An daɓa wa wanda aka kashen wuƙa a ciki, wanda ba tare da ɓata lokaci ba jami’an tsaro na Maidugurin suka ɗauke shi zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, inda jami’an lafiya suka tabbatar da rasuwarsa.
Wata majiyar ‘yan sanda ta ce, an kama wasu mutane bakwai masu shekaru tsakanin 15 zuwa 24.
Majiyar ta bayyana sunayen ababen zargin da aka kama da suka haɗa da Ba’abba Kyari mai kimanin shekara 20 sai Ali Alhaji Goni Ali dan shekara 20 da Muhammed Audu mai kimanin shekara 18, sai Ali Isa mai shekara 15 da Adam Sabir mai shekara 15 da Mohammed Tujja shekaru 17 da Usman Kasim dan shekara 24