‘Yar kasar ta Zimbabwe Kiristy Coventry ta zama mace ta farko daga fito daga nahiyar Afirka,kuma mace da za ta rike shugabannin hukumar wasannin Olympic.

An zabi Kirsty  ‘yan shekaru 41 ne a yayin kada kuri’a ta sirri da aka yi da ‘yan takara 7 su ka yi gogayya. An yi zaben ne ne a yayin taron hukumar ta Olympic karo na 144, a birnin Costa, Navarino a kasar Greece a jiya 20 ga watan nan na Maris.

Gabanin zabenta dai , Kirsty ta kasance wacce ta zama gwarzuwa ta iyo har sau biyu a wasannin Olympic.

Za ta fara aikin nata ne na shugabancin hukumar wasannin Olympic  a ranar 23 ga watan Yuni, da za ta gaji Thomas Bach dan kasar Jamus.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Nijar, Burkina Faso da Mali sun fice daga kungiyar kasashe renon Faransa

Kasashen Nijar da Burkina Faso da kuma Mali kowannensu sun sanar da ficewa daga kungiyar kasashe renon faransa ta (OIF).

Nijar ta sanar da ficewa daga kungiyar a ranar Litini, yayin da Mali ta bi sahu a ranar Talata, aa daidai lokacin da ake raya makon kungiyar.

Babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen kasar Laouali Labo, a wata wasika da ya aikewa jakadun kasar ya ce: “Gwamnatin Nijar ta yanke shawarar ficewa daga kungiyar ta OIF.”

Nijar dai na daga cikin kasashen da suka asassa kungiyar ta OIF, wacce aka kafa a Yamai babban birinin kasar a ranar 20 ga watan Maris na shekarar 1970, kuma tsohon shugaban kasar Dojori Hamani na waccen lokacin na daga cikin jagororin da suka kafa kungiyar.

To saidai dangankata ta yi tsami tsakanin faransa da sojojin dake mulki a kasashen guda uku a baya bayan nan.

Kungiyar ta OIF, “maimakon tallafawa wadannan kasashe wajen cimma manufofin raya al’ummarsu, (…) ta kauce wa hanya inda ta sanya siyasa a cikin lamuranta,” in ji ministocin harkokin wajen kawancen kasashen guda uku na Sahel a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a yammacin jiya Talata.

Kungiyar ta OIF, da ta hada kasashe da gwamnatoci 93, manufarta ita ce inganta harshen Faransanci da raya al’adu, don ƙarfafa zaman lafiya, da dimokuradiyya da ‘yancin dan adam, don tallafawa ilimi, horo da bincike, da kuma inganta hadin gwiwar tattalin arziki don samun ci gaba mai dorewa.

Sai nan da watanni shida masu zuwa ne ficewar kasashen za ta tabbata.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia
  • Manufofin Kasar Sin Sun Zamo Jagora Ga Duniya A Fannin Kare Hakkokin Bil Adama
  • Xi Ya Bukaci A Bude Sabbin Hanyoyin Samun Ci Gaba Yayin Rangadinsa A Lardin Yunnan
  • Kungiyar M-23 Ta Kasar Kongo Ta Kara Nusawa Gaba A Don Mamaye Karin Yankuna A Gabacin Kongo
  • A Jiya Laraba Ce Iran Take Bukukuwan Cika Shekaru 78 Da Kwatar Kamfanin Man Fetur Na Kasar Daga Hannun Turawan Burtaniya
  • MDD Ta Zargi Kasar Rasha Da Aikata Laifukan Yaki A Ukraine
  • Nijar, Burkina Faso da Mali sun fice daga kungiyar kasashe renon Faransa
  • Amurka ce Kadai Ta Ki Yin Allawadai Da Killace Gaza A Tsakanin Mambobin Kwamitin Tsaro na MDD
  • DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen Gwamna