Aminiya:
2025-03-22@03:35:03 GMT

Bam ya kashe mutum 4 da jikkata wasu a Borno

Published: 21st, March 2025 GMT

Aƙalla fasinjoji huɗu ne suka mutu yayin da wasu huɗu suka jikkata sakamakon fashewar wani bam a ƙarƙashin wata motar kasuwanci a ƙaramar hukumar Biu ta Jihar Borno.

Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta tabbatar ta afkuwar lamarin.

Gobara ta kashe ɗan shekara 7 a sansanin ’yan gudun hijira ’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe

Majiyoyin leƙen asiri sun shaidawa Zagazola Makama cewa, lamarin ya faru ne a ranar 19 ga Maris, 2025, da misalin ƙarfe 2:30 na rana a lokacin da wata mota ƙirar Golf 3 ta Wakil Fari ta tashi daga garin Kimba zuwa garin Biu.

Bayan sun isa mahaɗar Sabon Garin Kimba, motar ta taka wata nakiya (IED), wanda ya kai ga fashewa da ta kashe fasinjoji mata uku da fasinja namiji guda nan take.

Majiyar na cewar wasu fasinjoji hudu kuma sun sami raunuka daban-dabam kuma nan da nan an kai su babban asibitin Biu don yi musu jinya.

Daga bisani likitoci sun tabbatar da mutuwar wadancan mutane huɗu sannan aka ajiye su a ɗakin ajiyar gawa na asibitin kafin a miƙa su ga ’yan uwansu don yi musu jana’iza.

Bincike na farko ya nuna cewa ’yan ta’addar ISWAP ne suka dasa waɗannan bama-bamai (IEDs) a tunanin sojoji za su taka.

Jami’an soji sun tabbatar da faruwar hakan, tare da duba ƙarin barazanar da ake fuskanta daga wadannan ‘yan ta’addan don tabbatar da tsaro ga masu amfani da hanya.

Hukumomi sun kuma ƙaddamar da gangamin wayar da kan al’umma kan haɗarin bama-bamai da ba su fashe ba, don kaucewa faruwar lamari irin ya hakan.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Harin bam ISWAP

এছাড়াও পড়ুন:

Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 84, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 3 A Katsina

A cewar Kwamishinan, sojojin sun yi artabu da ‘yan ta’adda a kauyukan Malori da Matalawa, inda suka kara tura su cikin tsaunukan.

 

Mua’zu ya ci gaba da bayanin cewa, yayin da jami’an tsaron suka isa sansanin Sanusi Dutsin-Ma, sun yi nasarar tarwatsa jama’arsa tare da kashe ‘yan ta’adda uku, yayin da wasu da dama suka gudu da raunuka.

 

Bayan haka, sojojin sun ceto mutane 84 da aka yi garkuwa da su da suka hada da maza bakwai, mata 23, da kananan yara 54 da aka tsare a sansanonin ‘yan ta’addan.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gobara ta kashe ɗan shekara 7 a sansanin ’yan gudun hijira
  • Sojoji sun ceto mutum 84 da ’yan bindiga suka sace a Katsina
  • Wata Kotu A Abuja Ta Kori Karar Da Karuwai Suka Shigar Gabanta
  • An wawushe motar abinci ta Hukumar WFP a Borno
  • ’Yan Boko Haram 7 sun miƙa wuya ga sojojin MNJTF a Borno
  • Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 84, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 3 A Katsina
  • Sanƙarau ta kashe mutum 55 saboda rashin tsafta a Kebbi
  • Gobara ta kashe yara 3, ta jikkata 13 a Yobe
  • Wata Kungiya Mai Zaman Kanta Ta Samar Da Rijiyoyin Burtsatse A Karamar Hukumar Ringim