El-Rufa’i Ya Yi Kadan Ya Sa Mu Bar Jam’iyyar PDP – Sule Lamido
Published: 21st, March 2025 GMT
Lamido ya kasance tsohon sakataren jam’iyyar SDP, ya sake jaddada alkawarinsa ga PDP, yana mai cewa bai ga dalilin barinsa jam’iyyar ba.
Lokacin da na kasance sakataren jam’iyyar SDP, ina El-Rufai yake? Ina Shehu Gabam, shugaban jam’iyyar na kasa na yanzu? Duk da kalubalen da PDP ke fuskanta, a nan ne aka haife shi a siyasa.
Yana jaddada cewa El-Rufa’i ya samu nasara ne a siyasa ciki har da mukamin minista da ya rike sakamakon jam’iyyar PDP ne. A cewarsa, duk abin da ya mallaka a yanzu, ya samu ne ta sanadiyyar jam’iyyar PDP ne.
Lamido ya ce ya samu damar barin PDP ciki har da lokacin da jam’iyya suka yi hadaka wajen haifar APC a 2014, amma ya zabi ya ci gaba da zama a PDP. Ya ce wadanda suka bar jam’iyyar a baya sun yi haka ne saboda fushi, inda suka dunga aibata PDP, to amma yanzu me jam’iyyar APC ta yi musu?
Haka kuma, Lamido ya nanata cewa bai kamata a nemi shugabanci wajen bacin rai na kashin kai ba, shugabanci yana bukatar hakuri, juriya, yi wa al’umma hidima da kuma kasa gaba daya. Ya ce neman shugabanci ta hanyar fusata yana kasancewa ne ta kashin kai ba ta al’ummar kasa ba.
Ya yi gargadin cewa ka da a yi adawa da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta hanyar bukata ta kashin kai ko yin ramako. Ya ce idan manufar ita ce kawar da Tinubu kan karagar mulki, fushi ba shi ne hanya ba. Ya ce ya san yadda zai fuskanci adawa ta fusata.
Lamido ya yi kira a samar da shugabanci mai cike da adalci da kuma martaba hakkokin al’umma. Ya ce ya kamata a mayar da hankali wajen samar da shugabanci mai cike da adalci a Nijeriya maimakon nuna fushin siyasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Matatar Dangote Ta Dakatar Da Sayar Da Man Fetur A Naira
Matatar man Dangote ta sanar da dakatar da sayar da man fetur a naira. Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da matatar ta aika wa abokan huldarta a yammacin ranar Laraba. ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja El-Rufai Ya Shiga Tsilla-tsilla Bayan Rasa Kujerar Minista – APC A cikin sanarwar, Matatar ta ce, wannan matakin na wucin gadi ne, inda ta bayyana dalilin da ya sa aka dauki matakin domin samar da daidaito tsakanin farashin danyen mai da aka siyo da Dala da kuma na Naira. “Muna so mu sanar da ku cewa, matatar man Dangote ta dakatar da sayar da man fetur a Naira na wani dan lokaci domin kauce wa rashin daidaito tsakanin danyen man da ke wurinmu wanda a halin yanzu ke kan farashin dalar Amurka. “Ya zuwa yanzu, cinikin man fetur da muke samu a Naira ya zarce na danyen man da muka samu a farashin Naira, a sakamakon haka, dole ne mu daidaita kasuwancinmu na dan lokaci. “Muna ci gaba da jajircewa wajen ci gaba da bai wa ‘yan kasuwannin Nijeriya kayayyakinmu mai inganci da zarar mun samu danyen man fetur daga kamfanin NNPC, nan take za mu dawo da cinikin man fetur a Naira”.Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp