A cikin kwanaki 3 Falasdinawa 605 sun yi shahada a kisan kiyashin Isra’ila a Gaza
Published: 22nd, March 2025 GMT
Daruruwan Falastinawa fararen hula ne suka yi shahada tun bayan da Isra’ila ta dawo da hare-haren kisan kare dangi a kan al’ummar yankin zirin gaza, matakin day a yi hannun riga baki daya da yarejejeniyar dakatar da bude wuta da aka rattaba hannu a kanta karkashin jagorancin Amurka, Masar da kuma Qatar.
Dakarun mamaya na Isra’ila sun kaddamar da wani farmaki mai matukar muni da manyan makamai a ranar Juma’a a kan yankunan arewa maso yammacin Gaza da suka hada da Sudaniya, al-Karamah, da kuma Beit Lahia, wanda hakan ya yi sanadin shahadar fararen hula masu yawa da suka hada da mata da kananan yara, yayin da kuma wasu daruruwa suka jikkata.
Sojojin Isra’ila sun yi gargadi ga dukkanin Falasdinawa mazauna yankunan Sultan, Karama, da Awda da ke arewacin zirin Gaza, inda suka bukace su da su bar gidajensu, su koma zuwa yankunan kudancin Gaza.
Majiyoyin cikin gida sun ba da rahoton cewa, an kai wasu wadanda suka samu raunuka da dama da suka hada da wanda ke cikin mawuyacin hali zuwa asibitin Indonesiya da ke arewacin Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
MDD da EU sun yi tir da wargaza yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Isra’ila ta yi
Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai sun ce, tsagaita bude wuta nan take a Gaza ya zama dole.
Da yake magana a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, mataimakin babban sakataren majalisar kan harkokin siyasa Khaled Khari, ya ba da rahoto game da tabarbarewar al’amura a Gaza bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni da aka kwashe kusan watanni biyu ana aiki da ita.
“A kowace rana, muna kara nisa daga manufar mayar da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su zuwa gidajensu lami lafiya,” in ji Khari, yayin da yake magana kan fursunonin Isra’ila da aka yi garkuwa da su a Gaza.
Babban jami’in kula da harkokin siyasa na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a dawo da tattaunawar tsagaita bude wuta da kuma kai kayan agaji a Gaza ba tare da wata tangarda ba.
Ya yi ishara da jawabin da babban jami’in agaji na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher ya yi wa UNSC a farkon wannan makon, inda yace yin aiki da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ita ce hanya mafi dacewa domin kare fararen hula a Gaza, da kuma sako wadanda aka yi garkuwa da su, gami da shigar da kayan agaji da kayayyakin bukatar rayuwa zuwa Gaza.
Khari ya ce jami’an MDD shida na daga cikin daruruwan mutanen da aka kashe tun bayan da Isra’ila ta sake dawo da kai hare-hare a ranar Talata.
A daya bangaren kuma Majalisar Tarayyar Turai ta yi Allah wadai da “rugujewar yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkatar fararen hula masu yawa a hare-haren jiragen saman Isra’ila a baya-bayan nan”.
Har ila yau, ta bukaci komawa ga aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta nan take, tare da jaddada wajabcin ci gaba zuwa mataki na biyu na yarjejeniyar wanda Isra’ila ta yi fatali da shi.
Majalisar EU ta ce aiwatar da yarjejeniyar na da matukar muhimmanci wajen ganin an sako dukkan wadanda ake tsare da su a Gaza da kuma gidajen kurkukun Isra’ila, tare da cimma nasarar kawo karshen fada na dindindin.