Saree: Filin jirgin saman Ben Gurion ba shi da aminci har sai an kawo karshen yakin Isra’ila a Gaza
Published: 22nd, March 2025 GMT
Kakakin Rundunar Sojojin Yaman Birgediya Janar Yahya Saree, ya bayyana cewa, Dakarun Yemen sun harba makami mai linzami samfurin Falasdinu-2 a babban filin sauka da tashin jirgin saman Haramtacciyar Kasar Isra’ila na Ben Gurion.
Saree ya jaddada cewa, filin jirgin saman Ben Gurion ba shi da aminci ga zirga-zirgar jiragen sama, yana mai gargadin cewa za su ci gaba da kasancewa a fagen daga har sai Isra’ila ta kawo karshen yakin da take yi a kan al’ummar Gaza.
Tun da farko dai rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da cewa, an harba makamai masu linzami a yammacin jiya Juma’a a yankuna da dama da ke tsakiyar Falasdinu da ta mamaye, kuma Isra’ila ta tabbatar da cewa an harbo makaman ne daga kasar Yemen.
An ji karar fashewar wasu makamai masu linzami a sassan tsakiya na Falastinu da Isra’ila ta mamaye da hakan ya hada da kewayen birnin al-Quds. Kafofin yada labaran Isra’ila sun ba da rahoton dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a babban filin jirgin saman Ben Gurion sakamakon wadannan hare-hare na dakarun Yemen.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila ta
এছাড়াও পড়ুন:
Gaza: Sojojin HKI Sun Sake Kai Wa Asibitin “Ma’amadani Hari
Jiragen yakin HKI sun harba makamai masu linzami guda biyu akan ginin asibitin Ma’amadani dake Gaza. Harin ya yi sanadiyyar rushewar wasu bangarori da su ka hada dakunan yin gwaje-gwaje da kantin sayar da magani.
Saboda hare-haren na Isra’ila a wannan asibitin, da akwai gwamman marasa lafiya da suke kwance a kasa a waje, yayin da wasu kuma suke kwance wajen asibiti.
Kungiyar Hamas ta bayyana harin da sojojin HKI su ka kai wa asibitin da cewa wani sabon laifi ne na dabbanci da ‘yan sahayoniyar suka tafka a Gaza.
Haka nan kuma Kungiyar ta Hamas ta zargi Amurka da cewa ita ce take bai wa HKI haske akan tafka laifukan da take yi a Falasdinu.
Bugu da kari kungiyar ta Hamas ta kuma yi mamaki akan yadda kungiyoyin kasa da kasa da su ka hada da MDD suke yin shiru akan laifukan da ake tafkawa da ba su da tamka a wannan zamanin, akan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da cutar da marasa lafiya da korarsu daga asibiti zuwa kan tituna.