Aminiya:
2025-03-22@12:40:59 GMT

Dattawan Arewa sun buƙaci Tinubu ya dawo da Fubara kan kujerarsa

Published: 22nd, March 2025 GMT

Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da gaggauta janye dakatarwar da ya yi wa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, Mataimakiyarsa, da ’Yan Majalisar Dokokin jihar.

Da yake magana a madadin ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya ce babu wani dalili da ya dace da zai sa shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar.

Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia ’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe

Ya bayyana cewa, kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi ayyana dokar ta-ɓaci ne kawai a lokuta na matsanancin rikici kamar yaƙin basasa, ko rushewar doka da oda, wanda a cewarsa babu ɗaya daga cikinsu da ya faru a Jihar Ribas.

NEF, ta zargi Gwamnatin Tarayya da yin hakan ne saboda son rai, ba don amfanin al’umma ba.

Ƙungiyar ta yi zargin cewa rikicin siyasar yana da nasaba da taƙaddamar da ke tsakanin gwamnan da aka dakatar da tsohon gwamnan jihar wanda yanzu ministan Gwamnatin Tarayya ne.

Dattawan sun buƙaci gwamnati da ta dawo da dimokuraɗiyya, adalci, da zaman lafiya a Jihar Ribas.

Haka kuma, sun gargaɗi Gwamnatin Tarayya da kada ta bari irin wannan rikicin siyasa ya tsananta a wasu jihohi kamar Kano, inda ake ci gaba da samun saɓani dangane da masarautar Kano.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Dokar Ta Ɓaci Fubara gargaɗi Ƙungiyar Dattawan Arewa

এছাড়াও পড়ুন:

Ba Na Goyon Bayan Dakatar Da Gwamnan Jihar Ribas – Ndume

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Dokokin Nijeriya Ta Zama Ƴar Amshin Shata — Kwankwaso
  • Tinubu ya ba ni riƙon Ribas don wanzar da zaman lafiya — Ibas
  • Ba Na Goyon Bayan Dakatar Da Gwamnan Jihar Ribas – Ndume
  • Tinubu Ya Yaba Wa Majalisar Dokoki Kan Amincewa Da Dokar Ta-Ɓaci A Jihar Ribas
  • Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati
  • Majalisar wakilai ta amince da dokar ta-ɓaci a Ribas
  • Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa
  • Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Gwamnan Rikon Kwarya Na Jihar Rivers
  • Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya fice daga gidan gwamnatin Ribas