Iran da UAE sun kirayi Isra’ila da Amurka da su kawo karshen hare-harensu a Gaza da Yemen
Published: 22nd, March 2025 GMT
Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun bayyana matukar damuwarsu kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sake dawo da yakin kisan kare dangi a zirin Gaza da kuma hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar Yemen.
A wata tattaunawa ta wayar tarho a wannan Juma’a, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na UAE Abdullah bin Zayed Al Nahyan, sun tattauna batutuwan da suka shafi yankin, musamman ma ayyukan wuce gona da iri na Isra’ila a Gaza da kuma hare-haren Amurka a Yemen.
Araghchi ya yi kakkausar suka kan kisan gillar da gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi wa daruruwan Falasdinawa da ba su ji ba ba su gani ba tun daga ranar Talata, yana mai jaddada cewa yin hakan saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta ne da aka rattaba hannu a kansa.
Ya kuma yi Allah wadai da hare-haren da sojojin Amurka ke ci gaba da kai wa kasar Yemen, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mata da kananan yara da dama, tare da lalata muhimman ababen more rayuwa na yankin, da kuma jefa mutane cikin kangin talauci da yunwa.
Araghchi ya kara da cewa, laifuffukan da gwamnatin yahudawan sahyoniya ke aikatawa a Gaza da kuma harin da Amurka ta kai kan kasar Yaman na bukatar daukar matakin gaggawa da hadin gwiwa daga kasashen yankin da kum akasashen musulmi, domin dakatar da wannan ta’addanci da ke ci gaba da kawo rashin tsaro a duk fadin yankin gabas ta tsakiya.
A nasa bangaren, Ministan kasar UAE Abdullah bin Zayed ya bayyana matukar damuwarsa kan tabarbarewar al’amura a yankin, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin damuwa matuka.
Ya jaddada bukatar ci gaba da tuntubar juna tsakanin kasashen yankin domin hana ci gaba da tabarbarewar zaman lafiya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa sojojin Isra’ila sun zafafa kai hare-hare ta sama da kuma ta kasa a zirin Gaza tun daga ranar Talata, inda suke kai hari kan wuraren zaman jama’a da hakan ya hada da wuraren da aka tsugunnar da dubban mutane da suka rasa muhallansu da kuma gidaje, gami da asibitoci, tare da hana duk wasu ayyuka na jin kai ko ceton jama’a ko kai daukin gaggawa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Fadar Mulkin Amurka: Tattaunawa Da Iran Ta Yi Armashi
Fadar mulkin Amurka ta “White Hosue” ta bayyana cewa tattaunawar da aka yi a tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci da wakilin Donald Trump akan gabas ta tsakiya Steve Witkoff, ta hanyar shiga tsakanin kasar Oman, ta yi armashi.
Da marecen jiya Steve Witkoff ya bayyana cewa; shugaba Donald Trump ya ba shi umarnin ya yi duk abinda zai iya domin rage tazarar sabanin da ake da ita ta hanyar tattaunawa da diflomasiyya.
Bayanin na fadar mulkin Amurka ya kuma yaba wa kasar Oman wacce ta kasance mai masaukin baki na tattaunawar da aka yi wacce ba ta gaba da gaba ba ce a tsakanin Amurkan da kuma Iran.
Gabanin bayanin na fadar mulkin Amurkan, manzon musamman na shugaba Donald Trump, Steve Witkoff ya fada wa tashar talabijin din NBC cewa, ya yi tattaunawa mai matukar armashi da kuma amfani.
Tun a ranar Asabar da safe ne dai ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci ya isa birnin Mascut, inda ya gana da takwaransa na kasar Sayyid Hamad Bin Hamud al-Busa’idi, tare da mika masa bayanai da su ka kunshi mahangar Iran akan tattaunawar.
Ministan na harkokin wajen Oman ya zama mai shiga tsakanin kasashen biyu a tsawon lokacin tattaunawar. Bangarorin biyu sun yi musayar takardu har sau hudu.
A ranar Asabar mai zuwa ne dai za a ci gaba da tattaunawar daga inda aka tsaya a wani wurin da ba a kai ga ayyana shi ba.