Kasar Sin ta mika rijiyoyin burtsatsai 66 ga wasu yankunan lardin Mashonaland na gabashin Zimbabwe, wadanda za su samar da ruwa mai tsafta ga mutane kimanin 16,500.

Rijiyoyin wadanda kamfanin gine-gine na Geo-Engineering na kasar Sin ya gina, wani bangare ne na aikin hakar rijiyoyin burtsatsai 300 ga larduna 4 na kasar Zimbabwe.

Kasar Sin Ta Jaddada Bukatar Karfafa Cinikayya Da Ketare Tare Da Fadada Bude Kofa Masu Ruwa Da Tsaki Sun Gargadi Gwamnatin Tarayya Kan Samar Da Karin Jami’o’i

Yayin bikin mika rijiyoyin da aka yi jiya, ministan kula da kananan hukumomi da ayyukan more rayuwa na kasar Daniel Garwe, ya ce aikin alama ce ta hadin gwiwa da tausayi da goyon baya daga aminiyarsu a kowanne yanayi watau kasar Sin, wanda aka yi domin tabbatar da samar da ruwa mai tsafta ga kowa.

Shi kuwa jami’in kula da harkokin kasuwanci da tattalin arziki na ofishin jakadancin Sin a Zimbabwe Huang Minghai, cewa ya yi, aikin ya kara karfafa hadin gwiwar Sin da Zimbabawe da ya shafe gomman shekaru. Ya ce cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta gina rijiyoyin burtsatsai sama da 1,000 a fadin kasar ta Zimbabwe, wadanda mutane kusan 400,000 ke ci gajiyarsu. (Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: kasar Sin ta

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Sin Ta Jaddada Bukatar Karfafa Cinikayya Da Ketare Tare Da Fadada Bude Kofa

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Zabi ‘Yan Kasar Zimbabwe  Kuma Mace Ta Farko A Matsayin Shugabar Shugabar Kwamitin  Wasannin Olympic
  • Kasar Sin Ta Jaddada Bukatar Karfafa Cinikayya Da Ketare Tare Da Fadada Bude Kofa
  • An Yi Tarukan Tattaunawar Kasa Da Kasa Kan More Damammakin Sin A Havana Da Doha
  • Hajjin Bana: Dole A Yi Wa Maniyyatan Bauchi Riga-kafin Foliyo – Hukumar Alhazai
  • Shugaban Kasar Iran Ya Bukaci Hadin Kai Tsakanin Iraniyawa Saboda Amfanin Kasar
  • IAR da NAERLS Sun Shirya Taron Tattaunawa Da Masu Ruwa Da Tsaki Kan Noma Dawa A Najeriya
  • Manufofin Kasar Sin Sun Zamo Jagora Ga Duniya A Fannin Kare Hakkokin Bil Adama
  • Dokar Ta-Ɓaci: Tinubu Ya Kauce Hanya, Ya Ci Zarafin Dimokuraɗiyya A Ribas – Sambauna
  • Jami’i: Jiragen Saman Kasar Sin Za Su Bunkasa Sashen Sufurin Jiragen Afirka