Sin Za Ta Kara Daidaita Matakan Jawo Jarin Waje
Published: 22nd, March 2025 GMT
Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin He Yongqian, ta ce kasar za ta aiwatar da matakai na kara daidaita manufar jawo jarin waje a shekarar nan ta 2025, da aiwatar da matakan bude kofa a karin sassa, da kyautata yanayin kasuwanci a fannin.
He Yongqian, wadda ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a jiya Alhamis, ta ce ya zuwa yanzu kasar Sin ta baiwa wasu kamfanoni masu jarin waje 13 damar shiga hada-hadar inganta hidimomin wayar tarho, yayin da aka kaddamar da ayyuka masu jarin waje sama da 40 a fannin fasahar cin gajiya daga halittu masu rai.
Jami’ar ta kara da cewa a bana Sin za ta fadada sassan bude kofa a fannin ayyukan gwaji, wanda hakan zai mayar da hankali ga sassa kamar na raya ilimi da al’adu. Bugu da kari, a cewar jami’ar, ma’aikatarta ta taimaka wajen warware wasu batutuwa sama da 500, wadanda suka shafi kamfanoni masu jarin waje ta hanyar hawa teburin shawara, tana mai alkawarta aniyar kasar Sin ta ci gaba da aiki tukuru wajen inganta hidimomi, da yanayin gudanar da hada-hadar kasuwanci ga masu zuba jari na ketare. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: masu jarin waje
এছাড়াও পড়ুন:
MDD Ta Zargi Kasar Rasha Da Aikata Laifukan Yaki A Ukraine
Shugaban kwamiti na musamman dangane da yaki a Ukrai ya bayyana cewa kasar Rasha ta aikata laifukan yaki a yakin da take fafatawa a kasar Ukraine shekaru uku da suka gabata.
Shafin yanar gizo na Labarai, Africa News’ ya nakalto Erik Mose ya na fadar haka a taron kwamitin da yake jagoranra danagen da yaki a Ukraine a birnin Geneva a jiya Laraba.
Mose a fadawa kwamitin mai mutane 47 kan cewa, ya sami shaidu wadanda suke tabbatar da cewa a cikin shekaru uku da suka gabata gwamnatin kasar Rasha ta azabtar da wasu yan kasar Ukraine wadanda ta kama a yankuna guda 3 na Ukraine da ta kwace, kuma jami’an tsaron rasha sun azabtar da su, wasu kuma an yi masu piyade. Sannan wasu kuma an shigar da su cikin kasar Rasha, inda ba wanda ya san inda ake tsare da su. Tawagar kasar Rasha bata halarci taron kwamitin na jiya a birnin Geneva ba.