Sin Ta Ba Da Jawabi A Kwamitin Kare Hakkin Bil’adama Na MDD A Madadin Kungiyar Abokantaka Ta Inganta Hakkin Bil’adama
Published: 22nd, March 2025 GMT
Jakadan dindindin na kasar Sin dake ofishin MDD a birnin Geneva da sauran hukumomin kasa da kasa a kasar Switzerland, Chen Xu, ya gabatar da jawabi a madadin kungiyar abokantaka ta inganta hakkin bil’adama, da tattaunawa da hadin gwiwa da sauransu, yayin taron MDD karo na 58 da ya gudana a jiya Alhamis.
A cikin jawabinsa, jakada Chen ya bayyana damuwa game da mummunan tasirin da ra’ayin nuna bangaranci ya kawo, tare da tabbatar da bukatar aiwatar da ra’ayin cudanyar bangarori daban daban. Kazalika ya kamata a bi ka’idojin adalci, da gaskiya da kaucewa wariya a kwamitin kare hakkin bil’adama, ta yadda kare hakkin bil’adama zai gudana ta hanyar tsaro, da inganta hakkin bil’adama ta hanyar ci gaba, da kuma bunkasa hakkin bil’adama ta hanyar hadin gwiwa.
Dangote Zai Gina Sabuwar Masana’antar Siminti A Jihar Ogun Kasar Sin Ta Bayar Da Rijiyoyin Burtsasai 66 Ga Al’ummomin Zimbabwe Dake Fama Da Karancin RuwaJawabin nasa ya kunshi shawarwari guda uku na inganta ci gaban ayyukan kare hakkin bil’adama na duniya, inda da farko ya bukaci a tabbatar da gaskiya da adalci, sai na biyu dagewa wajen bude kofa, kana na uku shi ne tsayawa tsayin daka wajen samun nasara tare ta hadin gwiwa.
Bugu da kari, jawabin ya samu goyon bayan kasashe sama da 20, da suka hada da Rasha, da Cuba, da Eritrea da kuma Singapore, kuma kasashe masu tasowa sun yi tsokaci sosai a kan sa. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Abincin karnuka ya fi namu —Fursunonin Najeriya
Fursunoni a gidajen yarin daban-daban a sassan Najeriya sun koka game da munin irin abincin da ake ba su, wanda suka ce na karnuka ya fi shi.
Da dama daga cikin fursunonin da muka zanta da su sun bayyana cewa takwarorinsu sun sha mutuwa a sakamakon yunwa.
Wannan zargi na zuwa ne bayan da Hukumar Gidajen Yari ta Najeriya tare da wani kwamitin bincike mai zaman kansa sun ƙaryata zarge-zargen fursunonin kan yunwa a gidajen yari.
A watan Satumban 2024 ne Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya kafa a kwamitin domin gudanar da bincike kan zargin jami’an gidajen yari da cin hanci da kuma cin zarafin fursunonin.
NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar Edo NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar BornoDuk da cewa kwamitin ya tabbatar da zargin yunwa da fursunonin suka yi, Muƙaddashin Shugaban Hukumar Gidajen Yari ta Kasa, ya ce an zuzuta lamarin, saboda a cewarsa, babu alƙaluman da ke tabbatar da hakan.