Ribas: Ba mu karɓi sisin kwabo domin amincewa da dokar ta baci ba – Majalisar Wakilai
Published: 22nd, March 2025 GMT
Majalisar wakilai ta tarayya ta yi watsi da zargin da ake yi ga ‘yan majalisar tarayya na cin hanci da rashawa domin marawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu baya na ayyana dokar ta baci a jihar Ribas.
Dan majalisa mai wakiltar mazabar Gwaram daga jihar Jigawa, Honarabul Yusuf Shittu Galambi, ne ya kare majalisar a yayin da ake ta cece-kuce kan batun kafa dokar ta-baci a jihar Ribas, inda wasu kungiyoyi ke zargin majalisar dokokin kasar da yin kasa a gwiwa wajen yanke hukunci.
Sai dai, Galambi a wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar, ya ce babu gaskiya a ikirarin na cewa an tursasa ‘yan majalisar kan matakin da shugaban kasar ya dauka.
A cewarsa, yawancin mambobin sun goyi bayan matakin ne saboda ceto dimokuradiyya da kare muradun al’ummar jihar Ribas.
Dattawan Arewa sun buƙaci Tinubu ya dawo da Fubara kan kujerarsa
Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia
Dan majalisar ya bayyana cewa majalisar ta yanke shawarar ne bisa son tabbatar da kishin kasa, hadin kan siyasa, zaman lafiya, da kare dimokuradiyya.
“Na yi mamakin yadda kafafen yada labarai suka rika yada labaran karya, musamman kan zargin da ake yi mana, cewa mun an tilasta mana mu zartar da kudurin goyon bayan matakin da shugaban kasa ya dauka a jihar Ribas da kuma karbar daloli”
“Ya kamata ‘yan Najeriya su yaba da rawar da ‘yan majalisar dokokin kasar ke takawa wajen neman shugaban kasa ya kafa wata tawagar sasanta yan siyasa kafin karewar wa’adin dokar ta-baci na watanni shida.
Ya kuma jaddada cewa dole ne a kare dimokradiyya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fubara dokar ta baci jihar Ribas
এছাড়াও পড়ুন:
Dakatar da Gwamnan Ribas zubar da ƙimar Nijeriya ne a idon duniya — Jonathan
Tsohon Shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan ya ce dakatar da Gwamnan Ribas, Similanayi Fubara da aka yi kwanan nan zubar da ƙimar ƙasar ne a idon duniya.
Tsohon shugaban ya ce ba daidai ba ne dakatar da Gwamnan Ribas da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da ’yan majalisar dokokin jihar, wanda Shugaba Bola Tinubu ya yi a makon jiya.
An ayyana zaman makoki na kwana uku bayan kashe mutum 44 a Nijar An yi wa wata karya tiyatar ceton raiChannels TV ta ruwaito Jonathan yana bayyana haka yayin da yake jawabi a matsayin shugaban taro wanda gidauniyar Haske Satumari ta shirya a ranar Asabar a Abuja.
Jonathan wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa ne, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan matakin na cire zaɓaɓɓun shugabanni da aka yi.
“Wannan matakin da aka ɗauka zai ɓata sunan Nijeriya ne a idon duniya,” in ji shi.
Jonathan ya ce duk da cewar akwai buƙatar ɗaukar matakan da za su magance rikicin siyasar da ya dabaibaye Jihar Ribas na tsawon lokaci, a cewarsa dakatar da waɗanda mutane suka zaɓa a matsayin shugabanninsu bai dace ba.
Ya ƙara da cewa ya san bai kamata a matsayinsa tsohon shugaban ƙasa ya cika maganganu barkatai a game da abubuwan da suke a ƙasar ba, amma “yadda ake kallon Nijeriya yana ta’allaƙa ne a kan matakan ɓangaren zartaswa da majalisa da na shari’a suka ɗauka,” in ji shi.
A farkon makon da muka yi bankwana, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa dokar ta ɓaci a Jihar Ribas, ya kuma dakatar da gwamna da mataimakiyarsa da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.