Aminiya:
2025-03-22@19:55:06 GMT

Gwamnati ta kama mutum 347 kan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba

Published: 22nd, March 2025 GMT

Gwamnatin Tarayya ta kama mutum 347 da ake zargi da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a sassa daban-daban na Najeriya, inda aka gurfanar 143 a kotu.

Kama mutanen ya biyo bayan kafa wata runduna a shekarar 2024 don daƙile ayyukan haƙar ma’adanai ba ƙa’ida ba.

Kotun ƙoli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren PDP Kwankwaso ya yi Allah-wadai da ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas

Ministan Ma’adanai, Dele Alake, ya ce gwamnati na ƙoƙarin tabbatar da an hukunta mutum 327 da ke gaban kotu.

“A wannan watan, Babbar Kotun Tarayya da ke Ilorin ta yanke wa wasu ‘yan kasashen waje guda biyu, Yang Chao da Wu Shan Chuan, hukuncin ɗaurin gidan yari kan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

“Muna jinjina wa EFCC saboda ƙoƙarinta na gurfanar da masu aikata laifin,” in ji Alake.

Ministan ya ƙara da cewa runduna da aka kafa ta ƙwato wuraren haƙar ma’adanai guda 98, kuma ta gano wasu haramtattun wurare guda 457.

Gwamnati na shirin faɗaɗa ayyukan rundunar zuwa wasu jihohi tare da amfani da fasaha kamar jiragen sama marasa matuƙa da sauran na’urori don sanya ido.

“Rundunar ta ƙwace wuraren da wasu suka mamaye sama da shekaru 10 ba bisa doka ba.

“Wannan zai taimaka wajen bunƙasa kuɗaɗen shiga daga ɓangaren ma’adanai,” in ji shi.

Ministan ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ƙara yawan jami’an tsaro da kayan aiki domin daƙile ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

Ya gargaɗi duk masu aikata irin waɗannan laifuka da su daina, ko kuma su fuskanci hukunci.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Haƙar Ma adanai Karya Doka haƙar ma adanai ba bisa ƙa ida ba

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati

Sabon Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-ete Ibas (mai ritaya), ya isa jihar domin ci gaba da aiki.

Ibas ya isa filin jirgin saman Fatakwal da misalin ƙarfe 11:25 na safiyar ranar Alhamis inda ya samu tarba daga manyan jami’ai da jami’an tsaro.

’Yan Boko Haram 7 sun miƙa wuya ga sojojin MNJTF a Borno Majalisar wakilai ta amince da dokar ta-ɓaci a Ribas

Sabon Gwamnan, tare da rakiyar Kwamishinan ’yan sandan jihar, Olugbenga Adepoju da mataimakin babban sufeton ’yan sanda na shiyya ta 16, nan take suka wuce gidan gwamnati da ke Fatakwal.

Tuni dai Ibas ya isa gidan gwamnati inda wasu jami’an gwamnati suka zagaya da shi harabar gidan.

A yanzu haka yana ganawar sirri da manyan jami’an tsaro da wakilan gwamnatin tarayya da kuma jami’an gwamnatin jihar.

A ranar Talatar nan ne dai shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya naɗa Ɓice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas a matsayin kantoman jihar Riɓers bayan da ya sanar da ƙaƙaba wa jihar dokar ta-baci. Kuma ya rantsar da shi a ranar Laraba.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Bam ya kashe mutum 4 da jikkata wasu a Borno
  • Gwamnati Ta Jaddada ƙudirin Kare ‘Yancin Faɗin Albarkacin Baki Da ‘Yancin ‘Yan Jarida
  • An Bukaci Gwamnati A Kowani Mataki Da Ta Taimakawa Yaki Da Shan Magani Ba Bisa Ka’ida Ba
  • Araghchi : Iran za ta mayar da amsa ga wasikar Trump cikin kwanaki masu zuwa
  • Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati
  • ’Yan Boko Haram 7 sun miƙa wuya ga sojojin MNJTF a Borno
  • Cutar Sankarau Ta Kashe Mutane 56 A Kebbi
  • Farashin fetur na iya tashi bayan Dangote ya daina sayar da mai a Naira
  • Farashin fetur na iya tashi yayin da Dangote ya daina sayar da mai a Naira