HausaTv:
2025-04-14@16:22:48 GMT

An gudanar da gagarumar zanga-zangar nuna goyon bayan Falastinu a kasar Jordan

Published: 22nd, March 2025 GMT

Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza.

A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a.

Mahalarta tattakin sun yi Allah wadai da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan.

 A cikin wannan maci da aka gudanar bisa gayyatar Harkar Musulunci da kwamitin Tallafawa Falastinawa suka kira, dubban mutane sun halarta da suka hada da wakilai na siyasa, jam’iyyu, da kungiyoyin kwadago, da sauran jama’ar kasa, inda suka yi ta rera taken la’antar ayyukan zalunci na gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, da kuma kin amincewa da duk wata makarkashiyar da aka kulla domin korar Falastinawa daga yankunansu.

Haka nan Wadanda suka halarci tattakin sun yi Allah wadai da kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a zirin Gaza, tare da yin kira ga gwamnatocin kasashen Larabawa da na Musulunci da su dauki matakin gaggawa na dakatar da wannan aika-aikar da Isra’ila ke yi.

Mahalarta tattakin na nuna alhinin shahadar Abu Hamza, kakakin rundunonin Quds Brigade, sun yaba da karfin azamarsa da jajircewarsa, da sadaukar da ransa da jininsa saboda ‘yancin al’ummarsa.

Masu zanga-zangar sun kuma yi Allah wadai da cin amanar Amurkawa, wadanda suka bai wa makiya yahudawan damar soke yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma ci gaba da kashe al’ummar Gaza, tare da bayyana  gwamnatin Amurka a matsayin wadda take daukar nauyin wannan laifi ta hanyar aika bama-bamai da makamai masu linzami ga Isra’ila domin  kisan Falastinawa a zirin Gaza.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Allah wadai da

এছাড়াও পড়ুন:

CMG Ya Kaddamar Da Nuna Fina-Finai Da Shirye-Shiryen Talabijin Na Kasar Sin Masu Inganci A Malaysia

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Ce Za’a Gudanar Da Zagaye Na Gaba Tsakaninta Da Amurka Ne A Birnin Roma Na Kasar Italiya
  • CMG Ya Kaddamar Da Nuna Fina-Finai Da Shirye-Shiryen Talabijin Na Kasar Sin Masu Inganci A Malaysia
  • Jiragen Saman Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Luguden Wuta Kan Asibitin Baptist Da Ke Gaza
  • Al’ummar Mauritaniya Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Nuna Adawa Da Yakin Gaza
  • Gaza: Sojojin HKI Sun Sake Kai Wa Asibitin “Ma’amadani Hari
  • Sin Da Sifaniya Sun Daga Matsayin Hadin Gwiwa A Fannin Shirya Fina-finai
  • Sama da mutane 1,560 ne sukayi shahada tun bayan da Isra’ila ta koma kai farmaki Gaza
  • Isra’ila ta yi barazanar fadada hare-hare Gaza yayin da ta yanke Rafah daga birnin Khan Yunis
  • Sin Ta Yi Allah-wadai Da Karin Harajin Amurka Ta Kuma Jaddada Goyon Bayanta Ga Ka’idojin WTO 
  • Yemen Ta Maida Martani Kan Wasu Cibiyoyin Ajiyar Makamai A Yaffa Don Tallafawa Gaza