’Yan daba sun hallaka matashi ana sallar Tahajjud a Kaduna
Published: 22nd, March 2025 GMT
Wasu da ake kyautata zaton ’yan daba ne sun kai hari wani masallaci da ke yankin Rigasa a Jihar Kaduna, inda suka kashe wani matashi yayin da ake tsaka da sallar Tahajjud.
Sai dai rundunar ’yan sandan jihar, sun kama mutum 12 da ake zargi da hannu a kai hari masallacin.
Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia An wawushe motar abinci ta Hukumar WFP a BornoKakakin rundunar, Mansir Hassan, ya ce ’yan daban sun fito daga unguwanni daban-daban kamar Malalin Gabas, Tudun Wada, Rafin Guza, da Unguwar Baduko.
Sun kai farmaki Masallacin Layin Bilya, titin Makwa a Rigasa da misalin ƙarfe 2 na dare yayin da masu mutane ke sallar Tahajjud.
Kafin jami’an tsaro su isa wajen, sun sun daɓa wa wani matashi mai shekara 28, Usman Mohammed, wuƙa har lahira.
Rundunar tare da haɗin gwiwar JTF sun ɗauki mataki cikin gaggawa, inda suka kama mutum 12 kuma ana bincike a kansu.
Haka kuma, an samu makamai a hannu waɗanda aka kama.
An fara bincike domin gano gaskiyar lamarin da tabbatar da cewa an hukunta waɗanda suka aikata laifin.
Sakamakon haka, ’yan sanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a wuraren ibada da sauran wuraren da ake ganin za su iya fuskantar barazana.
Hukumomi sun buƙaci al’umma da su kasance masu sanya ido tare da gaggauta kai rahoto idan sun ga wani abun zargi.
’Yan sanda sun kuma gargaɗi masu aikata laifi da su daina ko su fuskanci hukunci mai tsanani.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hari Sallar Tahajjud Tudun Wada
এছাড়াও পড়ুন:
Hare-Haren Isra’ila Cikin Dare Sun Hallaka Mutum Aƙalla 50 A Gaza
Ƙungiyar bada agaji ta Civil defence a zirin Gaza ta ce hare-hare ta sama da Isra’ila ta kai cikin dare sun yi sanadin mutuwar mutum aƙalla 50 ciki harda yara ƙanana.
Hamas wadda zirin Gaza ke ƙarƙashin ikonta ta ce ta yi alla wadai da farmaki ta kasa na sojoji Isra’ila kuma ta bayyana shi a matsayin abinda ya saɓawa yajejeniyar tsagaita wuta na watanni biyu.
Rahotanni sun ce hare-haren da Isra’ila ta kai tun ranar Litinin wanda ya kawo ƙarshen yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da Hamas, sun shafi wata makaranta da ake tsugunar da waɗanda suka rasa muhalansu.
Tun da farko Ministan tsaron Isra’ila, Isreal Katz ya gargaɗi almummar Gaza akan cewa za a lalata yankin bakiɗaya idan ba su dawo da waɗanda aka yi garkuwa da su ba tare da katse duk alaƙa da Hamas.