Majalisar Wakilai ta musanta karɓar kuɗi kan dokar ta-ɓaci a Ribas
Published: 22nd, March 2025 GMT
Majalisar Wakilai ta ƙaryata zargin da ake mata na karɓar cin hanci domin amincewa da dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana a Jihar Ribas.
Ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Gwaram a Jihar Jigawa, Hon. Yusuf Shittu Galambi, ya kare majalisar yayin da ake ta cece-kuce kan batun.
Gwamnati ta kama mutum 347 kan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar NamibiaWasu ƙungiyoyi na zargin majalisar da yin ƙasa a gwiwa wajen yanke hukunci kan lamarin.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Galambi, ya ce babu gaskiya a zargin da ake yi cewa an tursasa ’yan majalisa ko an ba su na goro don su amince da matakin shugaban ƙasa.
Ya bayyana cewa yawancin mambobin majalisar sun goyi bayan matakin ne domin kare dimokuraɗiyya da kuma tsare muradun al’ummar Jihar Ribas.
“Mun yanke shawarar ne bisa kishin ƙasa, haɗin kan siyasa, zaman lafiya, da kare dimokuraɗiyya,” in ji shi.
Ya ce ya yi mamakin yadda wasu kafafen yaɗa labarai ke baza jita-jita cewa an tilasta musu su amince da dokar ta-ɓaci tare da karɓar daloli.
A cewarsa, ya kamata ’yan Najeriya su fahimci cewa ’yan majalisa suna aiki ne don ganin an samar da tawagar sulhu kafin wa’adin dokar ta-ɓacin ta ƙare.
Ya jaddada cewa dole ne a kare dimokuraɗiyya a Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dokar Ta Ɓaci Fubara Majalisar Wakilai Musantawa
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu Ta Dakatar Da INEC Karɓar Buƙatar Yin Kiranye Ga Senata Natasha
Kotun Tarayya da ke Lokoja, Jihar Kogi, ta bayar da umarnin dakatar da Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC) daga karɓar kowace buƙatar da aka gabatar domin fara shirin kiranye ga Senata Natasha Akpoti-Uduaghan daga Majalisar Dattawa.
Haka kuma, kotun ta hana ma’aikatan INEC, da wakilansu, ko duk wani wanda ke da hannu daga karɓar ko yin aiki da kowace buƙata da ke ɗauke da sunayen ƙarya daga mutanen mazaɓar Kogi ta tsakiya, sannan ta hana gudanar da kowanne zaɓe ko taro kan lamarin har sai kotu ta yanke hukunci.
Kwamitin Majalisa Ya Yi Watsi Da Ƙorafin Da Natasha Ta Shigar A Kan Akpabio Majalisar Dattawa Ta Dakatar Da Sanata Natasha Na tsawon Watanni 6 Saboda Rashin Da’aAn bayar da wannan umarnin ne bayan buƙatar gaggawa da Anebe Jacob Ogirima da wasu mutane huɗu daga yankin Kogi ta tsakiya, waɗanda suka yi rajista a matsayin masu zabe suka yi. Buƙatar ta samu wakilcin lauya Smart Nwachimere, na West-Idahosa, SAN & Co., inda kotu ta ɗage shari’ar zuwa 6 ga Mayu, 2025, don samun rahoton aikawa da gayyata da kuma ci gaba da sauraron shari’ar.
A cikin martani ga wannan hukunci, wata ƙungiya mai suna, Action Collective, ta yabawa kotu bisa wannan umarnin, inda shugaban ƙungiyar, Dr. Onimisi Ibrahim, ya ce wannan umarnin zai ƙara bayyana rashin biyayya daga wasu mutanen da ke goyon bayan shirin ƙoƙarin cire Natasha daga Majalisar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp