GMBNI Ta Yi Allah-wadai Da Kisan Gillar Wani Almajiri A Jihar Jigawa
Published: 22nd, March 2025 GMT
Wata kungiya mai suna Grassroots Mobilizers for Better Nigeria Initiative (GMBNI), ta yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa wani Almajiri a ƙaramar hukumar Gwaram, Jihar Jigawa.
Ƙungiyar ta bayyana matuƙar bakin ciki da ɓacin rai game da wannan cin zarafin da aka yi wa yaron, wanda ya kai ga mutuwarsa cikin mawuyacin hali.
A cewar jami’in yankin Arewa maso Yamma na kungiyar ta GMBNI, Abbas Rufa’i Wangara, rahotanni sun nuna cewa wani Malamin makarantar Allo ya yi wa yaron bulala da har ta kai ga mutuwarsa.
Lamarin ya ƙara muni inda ake zargin Malamin ya yanke kan gawar yaron, ya cire mazakutarsa gabansa na sirri, sannan ya binne gawar a wani ƙaramar rami.
GMBNI ta bayyana wannan aika-aika a matsayin cin zarafin ɗan Adam.
Ƙungiyar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan mamacin, tana mai jaddada cewa babu wani yaro da ya kamata ya fuskanci irin wannan zalunci, musamman a wurin da ake koyar da ilimi da tarbiyya.
GMBNI ta nanata buƙatar gaggawar yin gyara a tsarin ilimin Almajiranci, wanda ya daɗe yana fama da sakaci, cin zarafi, da rashin kulawa.
Ta yi kira ga hukumomi a dukkan matakai da su ɗauki matakan da suka dace don kare Almajirai tare da tabbatar da sun sami ingantaccen ilimi cikin kyakkyawar kulawa.
Ƙungiyar ta kuma bukaci hukumomin tsaro da na shari’a da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin, tare da tabbatar da cewa an hukunta wanda ya aikata wannan danyen aiki ba tare da ɓata lokaci ba.
Shugabar GMBNI, Ambasada (Dr.) Fatima Mohammed Goni, ta sake jaddada aniyar ƙungiyar na kare haƙƙin yaran da ke cikin mawuyacin hali.
Ta yi kira ga ƙungiyoyin farar hula, ‘yan kasa da al’ummar duniya baki ɗaya da su haɗa kai wajen neman adalci ga mamacin da kuma tashi tsaye wajen tabbatar da adalci da daidaito ga dukkan yara a Najeriya.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Ta Bukaci Taimakon NAMA Don Gudanar Da Aikin Hajjin Bana Cikin Nasara
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta roƙi Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA) ta ci gaba da ba da goyon baya domin tabbatar da nasarar gudanar da aikin Hajjin bana.
A ziyarar ayarin hukumar ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gudanarwa, Malam Baba Mohammed Rufa’i, wanda ya wakilci Shugaban Hukumar, Malam Salihu Abubakar, ta kai ziyara ga jami’an NAMA a Filin Jirgin Sama na Hassan Usman Katsina da ke Kaduna.
A yayin ziyarar, Malam Salihu Abubakar ya yaba wa NAMA bisa gudunmuwar da take badawa wajen nasarar hajjojin da suka gabata, inda ya roƙi irin wannan haɗin gwiwa a bana.
Ya jaddada muhimmancin samun ingantattun hanyoyin sufuri tare da roƙon NAMA ta tabbatar da samar da duk wani kayan aiki da ake bukata domin kauce wa cikas yayin jigilar alhazai.
A nasa jawabin, Manajan Harkokin Zirga-zirgar Jiragen Sama na filin jirgin, Alhaji AbdulMajid Mohammed, ya tabbatar da aniyar NAMA na ci gaba da tallafa wa aikin jigilar alhazan Jihar Kaduna.
Ya bayyana cewar har yanzu akwai matsalar ginin sabon hasumiyar kula da zirga-zirga da ba a kammala ba, yana mai ƙarin bayani cewa yawan katsewar wutar lantarki na kawo cikas, wanda ya sa yanzu filin jirgin ke aiki ne kawai kafin ƙarfe 5 na yamma.
Duk da waɗannan ƙalubalen, Alhaji AbdulMajid ya tabbatar wa Hukumar Jin Daɗin Alhazai cewa NAMA na da ƙudurinsa na ganin cewa aikin jigilar alhazan Kaduna zai kasance cikin tsari da kwanciyar hankali.
Ya tabbatar da cewa ana ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin rage yiwuwar samun cikas da kuma tabbatar da nasarar tafiyar Hajjin bana.
Rel/Adamu Yusuf