Za a hukunta ma’auratan da suka ci zarafin yarinya a kan mangwaro — Zulum
Published: 22nd, March 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Borno, ta ɗauki matakin hukunta wasu ma’aurata, Mamman Sheriff da matarsa, da aka kama suna cin zarafin wata yarinya a unguwar Pompomari Bypass da ke Maiduguri.
Bayan bayyanar faifan bidiyon da ya nuna ma’auratan suna dukan yarinyar, mutane da dama sun yi tir da abin a shafukan sada zumunta.
Wannan ya sa Hukumar Tsaron Sibil Difens (NSCDC) ta cafke su nan take.
Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da cewa gwamnati ba za ta musu sassauci ba.
Ya ce ma’aikatun shari’a, ilimi, da harkokin mata sun haɗa kai domin ganin an hukunta waɗanda suka aikata laifi.
Yarinyar, wacce ɗaliba ce, ta shiga harabar gidan ma’auratan domin tsinkar mangwaro bayan tashi daga makaranta, inda suka yi mata dukan kawo wuƙa.
A halin yanzu tana kwance a asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH), inda Dokta Lawan Bukar Alhaji ya ɗauki nauyin jinyarta.
Gwamnatin Borno ta kuma tallafa wa iyayen yarinyar da kayan agaji, abinci, da kuɗi.
Iyayenta da sauran jama’a sun yaba wa gwamnatin kan matakin da ta ɗauka na kare haƙƙin yarinyar.
Gwamnati ta jaddada cewa duk wanda aka kama da cin zarafin yara ba zai tsira daga hukunci ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: cin zarafi Ɗaliba gwamnati Ma aurata Mangwaro yarinya
এছাড়াও পড়ুন:
Idris Ya Musanta Rahoton Wai Ya Ce A Yi Watsi Da Koken Gwamna Zulum Kan Rashin Tsaro A Borno
Ministan ya ce maganar da ya faɗa da farko wadda ba a ruwaito ta a daidai ba ita ce:
“E, lallai an samu cigaba a harkar tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan, ko da yake ba a kawar da duk wani aikin tashin hankali gaba ɗaya ba.
“Hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana don tabbatar da cewa an shawo kan matsalolin da ake da su a wasu sassan Jihar Borno da wasu wurare.
“Haɗin gwiwar da muke gani tsakanin hukumomin tsaro, musamman a shekaru biyu da suka wuce, da kuma gagarumin zuba jari a kayan aiki da na’urorin zamani da ake yi, yana nuna yadda Gwamnatin Tarayya take ɗaukar batun tsaro da matuƙar muhimmanci.
“Gwamnatin Tinubu tana da ƙwarin gwiwar kawar da ayyukan ‘yan bindiga da ta’addanci a faɗin ƙasar.
“Nasarorin da hukumomin tsaro suka samu a cikin watanni 18 da suka wuce suna nuna cewa lallai Nijeriya tana komawa daidai a hankali a hankali.
“Gwamnati tana kira ga kowa da kowa, musamman gwamnatocin jihohi, da su haɗa hannu wajen kawar da ragowar ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka a duk inda suke.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp