Ya kuma kara da cewa dorewar tsarin dimokiradiyya na bukatar hadin gwiwa daga kowane bangare, “Jam’iyyun siyasa su ne ginshikin dorewar dimokiraɗiyya, kuma yayin da hamayya take da muhimmanci a lokacin zabe, dole ne mu hada kai wajen gina kasar mu, hakan ya sa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda babban jami’in dimokiradiyya ne yake mutunta gasa mai tsafta, amma kuma ya na fifita hadin kai da ci gaban kasa fiye da komai.

Shugaban IPAC na kasa, Honourable Yusuf Dantalle, ya ce shirin fim din na tarihi zai bayyana ci gaban da aka samu a fannonin gina ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da hadin kan al’umma, ya kuma ci gaba da “Fim din zai zama wani muhimmin tarihin kasa, zai kuma mayar da hankali kan matasa, musamman ‘yan zamani (Gen Z), domin ya zama wata hanyar ilmantarwa da hade kan ‘yan kasa domin su kara sanin abinda ake nufi da Dimokuradiyya a Nijeriya.

Fim din zai kunshi fitattun jaruman Nollywood kuma za a shirya shi da na’urori na zamani domin ya dace da matakin inganci na duniya, ta yadda babu wani wanda zai kalla ba tare da ya yaba wa wadanda su ka dauki nauyin shirya wannan kasaitaccen shiri.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Chelle Ya Fara Da Ƙafar Dama A Super Eagles 

Sabon Kocin tawagar Super Eagles ta Nijeriya Eric Chelle, ya fara jagorantar tawagar da ƙafar dama, bayan samun nasara a wasan farko da ya jagorance ta.

Chelle wanda ya zo Super Eagles watanni biyu da su ka gabata, ya jagoranci Super Eagles a wasan da su ka doke ƙasar Rwanda da ci biyu da nema a Amahoro.

Wasan shi ne zagaye na biyar a wasannin neman gurbi a gasar cin kofin Duniya da za a buga a shekarar 2026, Nijeriya na matsayi na 4 a rukunin C na gasar da maki 6 a wasanni 5, sai Afrika Ta Kudu dake jan ragamar rukunin, ƙasar Benin ta biyu sai Rwanda dake matsayi na uku.

Eric Chelle Ya Sake Bai Wa Ahmed Musa Damar Taka Leda A Super Eagles Ministan Harkokin Wajen Benin Ya Yi Wa Sinawa Gaisuwar Sabuwar Shekara

Tsohon gwarzon ɗan wasan Afrika Victor Osimhen ne ya jefa wa Nijeriya duka kwallayenta biyu a wasan, Ademola Lookman da Samuel Chukwueze ne su ka taimakawa Osimhen wajen zura kwallayen a ragar masu masaukin bakin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wang Yi: Kasar Sin Na Da Kwarin Gwiwa Kan Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Japan Da Koriya Ta Kudu  
  • Hikimar Gwamnatin Jihar Jigawa Na Kaddamar Da Shirin Gina Rijiyoyin Burtsatsan Noman Rani
  • Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da shirin noman rani na Lallashi
  • Dalilan Gwamnatin Tarayya Na Zuba Naira Tiriliyan 1.5 A Bankin Aikin Noma -Kyari
  • Chelle Ya Fara Da Ƙafar Dama A Super Eagles 
  • Ribas: Ba mu karɓi sisin kwabo domin amincewa da dokar ta baci ba – Majalisar Wakilai
  • Najeriya: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da Zargin Kisan Kiristoci A Kasar
  • An Bukaci Shugaban Kasa Ya Sa Ido Ga Aikin Biyan Kudaden Fansho
  • Zargin Kisan Kiristoci A Nijeriya: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da Rahoton Amurka