Chelle Ya Fara Da Ƙafar Dama A Super Eagles
Published: 22nd, March 2025 GMT
Sabon Kocin tawagar Super Eagles ta Nijeriya Eric Chelle, ya fara jagorantar tawagar da ƙafar dama, bayan samun nasara a wasan farko da ya jagorance ta.
Chelle wanda ya zo Super Eagles watanni biyu da su ka gabata, ya jagoranci Super Eagles a wasan da su ka doke ƙasar Rwanda da ci biyu da nema a Amahoro.
Wasan shi ne zagaye na biyar a wasannin neman gurbi a gasar cin kofin Duniya da za a buga a shekarar 2026, Nijeriya na matsayi na 4 a rukunin C na gasar da maki 6 a wasanni 5, sai Afrika Ta Kudu dake jan ragamar rukunin, ƙasar Benin ta biyu sai Rwanda dake matsayi na uku.
Eric Chelle Ya Sake Bai Wa Ahmed Musa Damar Taka Leda A Super Eagles Ministan Harkokin Wajen Benin Ya Yi Wa Sinawa Gaisuwar Sabuwar ShekaraTsohon gwarzon ɗan wasan Afrika Victor Osimhen ne ya jefa wa Nijeriya duka kwallayenta biyu a wasan, Ademola Lookman da Samuel Chukwueze ne su ka taimakawa Osimhen wajen zura kwallayen a ragar masu masaukin bakin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Yaffa Kusa Da Tel Aviv A Karo Na Biyu A Cikin Sa’o’i 24
Sojojin kasar Yemen sun cilla makami mai linzami samfurai Balistic kuma Hypersonic kan birnin Yafa kusa da Telaviv a cikin HKI karo na biyu a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata. Harin dai yana daga cikin manya-manyan hare-haren da sojojin na Yemen suka kai kan HKI tun bayan sake komawa yaki tufanul Aksa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar ta Yemen Burgediya Janar Yahya Saree yana bada sanarwan kai harin, a jiya Alhamis ya kuma kara da cewa, hari mai kyua wanda ya dace da tallafawa Falasdinawa a Gaza.
Saree ya kammala da cewa matukar sojojin HKI sun ci gaba da kissan kiyashin da suke yi a Gaza