Dakatar da Gwamnan Ribas zubar da ƙimar Nijeriya ne a idon duniya — Jonathan
Published: 22nd, March 2025 GMT
Tsohon Shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan ya ce dakatar da Gwamnan Ribas, Similanayi Fubara da aka yi kwanan nan zubar da ƙimar ƙasar ne a idon duniya.
Tsohon shugaban ya ce ba daidai ba ne dakatar da Gwamnan Ribas da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da ’yan majalisar dokokin jihar, wanda Shugaba Bola Tinubu ya yi a makon jiya.
Channels TV ta ruwaito Jonathan yana bayyana haka yayin da yake jawabi a matsayin shugaban taro wanda gidauniyar Haske Satumari ta shirya a ranar Asabar a Abuja.
Jonathan wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa ne, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan matakin na cire zaɓaɓɓun shugabanni da aka yi.
“Wannan matakin da aka ɗauka zai ɓata sunan Nijeriya ne a idon duniya,” in ji shi.
Jonathan ya ce duk da cewar akwai buƙatar ɗaukar matakan da za su magance rikicin siyasar da ya dabaibaye Jihar Ribas na tsawon lokaci, a cewarsa dakatar da waɗanda mutane suka zaɓa a matsayin shugabanninsu bai dace ba.
Ya ƙara da cewa ya san bai kamata a matsayinsa tsohon shugaban ƙasa ya cika maganganu barkatai a game da abubuwan da suke a ƙasar ba, amma “yadda ake kallon Nijeriya yana ta’allaƙa ne a kan matakan ɓangaren zartaswa da majalisa da na shari’a suka ɗauka,” in ji shi.
A farkon makon da muka yi bankwana, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa dokar ta ɓaci a Jihar Ribas, ya kuma dakatar da gwamna da mataimakiyarsa da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Ribas Siminalayi Fubara
এছাড়াও পড়ুন:
Yaya ‘Yan Siyasar Amurka Ke Kasafta Harajin Ramuwar Gayya?
Manufar “ramuwar gayya” ba za ta daidaita gibin cinikin da kasar Amurka take fuskanta ba, illa ta daga farashin kayan da ake shigarwa kasar daga kasashen waje, da haddasa hadarin hauhawar farashin kaya a kasar, da kawo illa ga zaman rayuwar jama’ar kasar. A karshe Amurka ba za ta cimma burinta na zama a matsayin koli a duniya ba. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp