Kwana Daya Bayan Kwace Fadar Shugaban Kasa, Sojojin Sudan Sun Kwace Babban Bankin Kasar
Published: 22nd, March 2025 GMT
A ci gaba da shimfida ikonsu da suke yi a cikin birnin Khartum, sojojin Sudan sun kwace iko da babban bankin kasar, kwana daya bayan da su ka kori dakarun kai daukin gaggawa daga fadar shugaban kasa.
Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya nakalto majiyar sojojin Sudan tana cewa; A yau Asabar sun yi nasarar kwace iko da babban bankin kasar, tare kuma da shimfida ikonsu a cikin wasu yankunan na birnin Khartum.
Kakakin sojan kasar Sudan Nabil Abdullah, ya bayyana cewa; Mun rusa sojoji da kayan aikin abokan gaba. Haka nan kuma Abdullah ya sanar da kwace wasu ma’aikatu da suke a tsakiyar birnin Beirut da su ka kasace a karkashin ikon dakarun kai daukin gaggawa.
Ana zargin rundunar kai daukin gaggawa da tafka laifukan yaki a cikin yankunan da a baya su ka shimfida ikonsu a ciki, har da babban birnin kasar Khartum.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
HKI: Ana Samun Koma Bayan Sojojin Sa-Kai Da Suke
Jaridar “Yediot-Ahranot” ta buga wani rahoto da yake kunshe da gargadi daga jami’an sojan mamaya akan yadda ake samun koma baya na sojojin sa-kai saboda da dalilai mabanbanta.
Daga cikin dalilan da jaridar ta bijiro da su da akwai gajiya da yaki na lokacin mai tsawo da HKI ta shiga, sai kuma matsaloli na tattalin arziki da kashe kudade masu yawa wajen kula da su.
Haka nan kuma manyan jami’an sojan mamayar sun bayyana yiyuwar rusa rundunar sojan sa-kai din saboda babu wadanda su ka dace su jagorance ta, ga kuma tsadar tafiyar da rundunar kamar yadda jaridar ta “Ahranot” ta bayyana.
Ita kuwa jaridar “Financial-Times” ta bijiro da tata majiyar da take cewa; Yakin da ba shi da ranar karewa da Isra’ila take yi, ya gajiyar da sojojin sa-kai.
Wani sashe na rahoton jaridar ya ambaci cewa; Tare da cewa yarjejeniyar da aka yi da sojojin sa-kai din shi ne cewa a cikin shekara daya za su yi yakin kwanaki 30 ne kadai,amma kuma yanzu an sanar da iyalansu cewa, su kasance cikin shirin yin yaki babu kakkautawa har na tsawon shekaru masu yawa.
Jaridar ta “Financial Times” ta kuma ce ‘yan sahayoniyar suna da bukatar Karin sojoji 10,000 saboda kara tsaro, a yankunan da suke kusa da Gaza.
HKI tana da cikakkun sojoji170,000 sai kuma sojojin sa-kai da su ka kai 465, a 2024 kamar yadda shafin :Global Fire Power” ya ambata.