Amurka: Turmp Yana Son Yin Yarjejeniya Ne Da Iran Ba Yaki Ba!
Published: 22nd, March 2025 GMT
A wata hira da tashar talabijin din, manzon musamman na Amurka a yankin gabas ta tsakiya Steve Witkoff ya rubuta a shafinsa na; X cewa; Sakon da Trump ya aike wa Tehran ba ta nufin yin barazana.
Manzon na Amurka ya riya cewa;wasikar ta kunshi cewa; Ni shugaban kasa ne mai son zaman lafiya , abinda nake son bayyanawa kenan, don haka babu bukatar a yi magar yaki.
Wittkoff ya kuma ce; Da akwai hanyoyi na bayan fage da ake tatatunawa da Iran.
Har ila yau ya kara da cewa; Abinda Trump yake so shi ne warware sabanin da ake da shi.
Shafin watsa labaru na Axos ya bayyana cewa; Waskiyar da Trump din ya aiko wa Iran ta kunshi ayyana wa’adin watanni biyu na cimma sabuwar yarjejeniya Nukiliya.
Wannan sabon matsayin na Amurka dai ya zo ne,bayan da mahukunta a jamhuriyar musulunci ta Iran suka bayyana cewa; Amurkan ba za ta sami wani abu daga Iran ba ta hanyar barazana.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Dole Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Ta Daina Barazana Ga Masu Sukar Ta – Amnesty
Kungiyar ta ce a maimakon neman cin mutuncin Uguamaye kamata ya yi gwamnatin tarayya ta dukufa neman kawo sauyin da zai rage wa jama’a wahalhalun da suke fuskanta da magance matsalolin tattalin arziki da kasar ke ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp