KAmfanin dillancin labarun “al-Somariyya Newas” ya ambato jagoran ‘yan hamayyar siyasa na kasar Turkiya Uzgor Auzal yana fadin cewa: A daren jiya juma’a adadin wadanda su ka fito Zanga-zangar nuna kin jinin shugaba Rajab Tayyib Urdugan sakamakon sauke da kama ‘yan hamayyar siyasa da ya yi kaga kan mukamansu da su ka hada da magajin garin birnin  Istanbul.

Magajin garin Istanbul Imam Uglu ya yi watsi da duk wata tuhuma da aa yi masa ta hannu a cin hanci da rashawa.

Kamfanin dillancin labaran “Reusters” ya nakalto wata majiyar shari’a tana cewa Imam Uglu ya yi watsi da dukkanin thume-tuhumen da aka yi masa masu alaka a cin hanci da rashawa.

Shi dai Imam Uglu zai tsaya takarar shugabancin kasa da Urdugan, kuma ana tsinkayo cewa zai iya lashe zabe.

Jami’ar adawa da Imam Uglu ya fito daga cikinta “ Turkish Republican Party” ta yi Allawadai da kama Imam Uglu, tare da bayyana shi da cewa, bi ta da kulli ne na siyasa kawai.

Bayan kama Imam Uuglu Zanga-zanga ta barke a cikin birane da garuruwa mabanbanta na kasar ta Turkiya  tare da yin tir da abinda ya faru.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Babu ’yan adawan da za su iya hana Tinubu lashe zaɓen 2027 — Ganduje

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa babu wata gamayyar ’yan adawa da za ta iya hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu lashe wa’adi na biyu a zaɓen 2027.

Ya yi wannan jawabi ne domin mayar da martani ga sabuwar haɗakar ’yan adawa da Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da wasu shugabanni suka kafa.

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika Alƙawari Majalisar wakilai ta amince da dokar ta-ɓaci a Ribas

A yayin taron manema labarai da Atiku ya gudanar a Abuja a ranar Alhamis, ya soki yadda Tinubu ke tafiyar da mulki, musamman batun ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas.

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha, da wasu ’yan siyasa sun hallara, inda suka bayyana shirin haɗa kai domin karɓe mulki daga hannun Tinubu a 2027.

Sai dai Ganduje ya yi watsi da wannan yunƙuri, inda ya bayyana cewa tafiyar ba za ta yi tasiri ba.

“Babu wata yarjejeniya ko haɗa kai da za ta hana ’yan Najeriya sake zaɓen Tinubu a 2027,” in ji shi a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan wayar da kan jama’a, Cif Oliver Okpala, ya fitar.

Ya ce irin nasarorin da Tinubu ya samu tun bayan hawansa mulki ne zai tabbatar da nasararsa.

“Tabbas Tinubu zai sake lashe zaɓe saboda irin ci gaban da ya kawo tun bayan da ya zama shugaban ƙasa,” in ji Ganduje.

Haka kuma, ya ce wannan sabuwar haɗakar ’yan adawa ba za ta yi tasiri ba, domin ’yan siyasar da ke ciki na da manufofi daban-daban.

“Ku manta da waɗannan tarukan na ‘yan siyasa da maganganunsu marasa tushe, domin yawancinsu ba su da wata makoma ta siyasa,” in ji shi.

“Haɗin gwiwarsu – kama daga kan jam’iyyar LP zuwa PDP da SDP – na ƙunshe da mutanen da ke da ra’ayoyi daban-daban da kuma son zuciya. Ba za su taɓa iya cimma muradi na siyasa ba.”

Wannan martani na Ganduje na nuni da cewa zaɓen 2027 zai kasance mai ɗaukar hankali tare da fafatawa mai zafi tsakanin ɓangarorin siyasa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fiye Da Dalibai 4,200 Suka Amfana Da Tallafin Ilimi Na Sanata Solomon Adeola
  • Isra’ila ta kashe wani mamba na ofishin siyasa na Hamas
  • Isra’ila : ‘Yan adawa sun kira zanga-zangar gama-gari bayan korar shugaban Shin Bet
  • An gudanar da gagarumar zanga-zangar nuna goyon bayan Falastinu a kasar Jordan
  • Taƙaddama: An kama wanda ya daɓa wa matarsa ​​wuƙa ta mutu
  • Tinubu ya ba ni riƙon Ribas don wanzar da zaman lafiya — Ibas
  • Dubban Mutane Sun Fito Zanga-Zangar Yin Allawadai Da Kama Magajin Garin Istambul
  • Babu ’yan adawan da za su iya hana Tinubu lashe zaɓen 2027 — Ganduje
  • ’Yan adawa sun shirya ƙalubalantar Tinubu a zaɓen 2027 – Atiku