Mutumin da girgizar ƙasa ta razana ya shekara 2 yana zaune a cikin kogo
Published: 23rd, March 2025 GMT
Wani ɗan ƙasar Turkiyya da ya rasa gidansa sakamakon wata gagarumar girgizar ƙasa a shekarar 2023, ya shafe shekara biyu yana zaune shi kadai a cikin wani ƙaramin kogo saboda yana ganin ya fi kowane gini da mutum zai yi karko.
A watan Fabrairun 2023, Kudancin Turkiyya ya fuskanci ibtila’in girgizar kasa mai karfin 7.
Ali Bozoğlan, mahaifin ‘ya’ya uku daga lardin Hatay da ke kudancin kasar, ya rasa gidansa sakamakon girgizar kasar da aka yi a ranar 6 ga watan Fabrairu 2023.
Duk da cewa shi da iyalinsa sun tsira ba tare da wata matsala ba, Ali ya firgita da girgizar kasar har ya yanke shawarar ba ya son zama a ginin da mutum ya yi.
Maimakon haka, sai ya sami wani karamin kogo da zai iya zama lafiya a wajen birnin, inda ya mayar da shi gida.
Kodayake ya kasa shawo kan iyalinsa su hadu da shi don zama a cikin kogon da ba a saba gani ba, sai dai ya yi ikirarin cewa yana farin ciki kuma yana cikin kwanciyar hankali a inda yake.
Ali Bozoğlan ya shaida wa kafar yada labarai ta TGRT Haber cewa, “Na shafe shekara 2 ina zaune a nan bayan girgizar kasar kuma na sami kwanciyar hankali a cikin wannan kogon.
“Wannan kogon ya wanzu tsawon dubban shekaru kuma bai rushe ba.”
Bayan da an samu labarin yadda mutumin yake rayuwa, sai Hakimin Defne ya ba shi wata kwantenar gida mai kyau a wani wuri kusa da birnin, amma Ali ya so ya nisantar da kansa da birni mai cike da cunkoson jama’a, domin ya saba da rayuwar kwanciyar hankali a cikin karamin kogon nasa.
“Ina wanke kwanukan abincina da yin wanki da kuma yin abincin da zan ci. Ina yin kyakkyawar rayuwa a cikin kogon,” in ji Ali.
“Ba ni da kowa kuma ina hulda da yanayi. Mutanen da ba su da ilimi suna yin munanan maganganu game da rayuwata a cikin kogon.
“Domin ba sa zama da ni, suna magana da ni, kuma ba su san ni ba, suna yin kalamai daban-daban.”
Ali ya yarda cewa zama shi kadai a cikin kogo bai dace ba. Domin wuri ne mai zafi sosai a lokacin hunturu da sanyi da rani, yana jawo macizai da beraye, amma duk da haka ya saba da shi.
Haka kuma ya so ya sami ya rika shiga bandaki da samun ruwan sha, amma ba zai yiwu ba.
Yanzu ya shirya saka na’urorin samar da lantarki ta hasken rana domin ya iya sarrafa injin wanki da firinjinsa, amma ko da mafarkinsa bai zama gaskiya ba, ba zai yi watsi jin dadin kogon nasa ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Girgizar kasa Turkiyya
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato
Rahotanni sun ce an kashe wani uba da ‘ya’yansa biyu a ƙauyen Zogu da ke Gundumar Miango a Ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.
Kakakin Ƙungiyar ci gaban Irigwe (IDA), Sam Jugo, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Jos, ya bayyana sunayen waɗanda harin ya rutsa da su kamar haka, Weyi Gebeh a mai shekara 56, da Zhu Weyi mai shekara 25 da Henry Weyi mai shekara 16.
‘Tell Your Papa’: NBC ta haramta amfani da waƙar da ke sukar Tinubu An kama mutum 8 kan faɗan daba a KanoA cewar Jugo, an kashe mutanen ne cikin dare a lokacin da suke barci, inda ya bayyana lamarin a matsayin dabbanci.
Ya ce, “An sanar da shugabannin Ƙungiyar ci gaban Irigwe (IDA) game da wani harin da aka kai ƙauyen Zogu, Miango wanda ya yi sanadin mutuwar wani uba da ‘ya’yansa biyu waɗanda suka haɗa da: Weyi Gebeh da Zhu Weyi da Henry Weyi.
“Wannan harin na baya-bayan nan ya kai ga mutuwar mutane tara a cikin makon nan kaɗai, Ƙungiyar IDA ta nuna rashin jin daɗinta game da taɓarɓarewar al’amura a yankin Irigwe tare da yin kira ga jami’an tsaro da su yi duk abin da ya kamata don daƙile wannan ɓarna a yankinmu tare da kama waɗanda suka aikata laifin don fuskantar shari’a.
Kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ Manjo Samson Zhakom da rundunar ’yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, har yanzu ba su mayar da martani ga saƙon da wakilinmu ya aika masu ba.